Tanka Makare da Gas Ta Fadi a Legas, An Shiga Aikin Ceto domin Kare Rayuka
- Wata tanka cike da silindar gas ta kife a tsakiyar titin babban titin Anthony One, Oshodi-Apapa da ke jihar Legas
- Lamarin ya jefa jama'a cikin tsoro ganin hadarin irin kayan da tankar ke dauke da shi, amma jami'an agaji sun isa wurin
- Hukumar kula da ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA) ta bayyana cewa jami'anta sun hallara tun tuni
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Masu ababen hawa da ke bin titin Anthony Oke zuwa Gbagada ta babbar hanyar Oshodi-Apapa sun tsallake rijiya da baya yayin da tanka dauke da gas ta fadi.
Lamarin ya jawo fargaba da karin cunkoson ababen hawa da ke bin babban titin, sai dai lamura sai daidaita da wuri.
A sanarwar da hukumar LASTMA ta wallafa a shafin X, an gano mutum daya da ya ji rauni a hannunsa, wanda aka tabbatar da cewa shi ne matukin motar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga jami'an LASTMA, an samu karin jami'an agaji da su ka isa wurin domin aikin ceto da kuma hana hadarin ya kara muni.
Babu asarar rai a hadarin Legas
Hukumar kula da hanya ta Legas ta bayyana cewa ba a samu asarar rai a kifewar tankar gas ba da ya afku a jihar, Premium Times ta wallafa.
Darakta a sashen wayar da kan jama'a na hukumar, Adebayo Taofiq ya bayyana cewa aikin ceton gaggawa da jami'ansu su ka kai ya dakile karuwar illar hadarin.
Ya kara da cewa tuni su ka yi nasarar dauke tankar da gas din da ta ke dauke da shi, kuma an ci gaba da zirga-zirga a hanyar kamar yadda aka saba.
Hadarin mota ya jawo asarar rayuka
A baya mun ruwaito cewa wani hadarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar maza 11 yayin da karamar mota ta yi karo da wata tirela a Zariya, jihar Kaduna.
Hukumar kare afkuwar hadurra a jihar, Kabir Nadabo ya bayyana cewa motoci kan bi hannu daya a yankin Gwargwaje, daidai inda hadarin ya afku.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng