Yar Majalisa Ta ce Ita ma Tana Jin Yunwa, Ta Fadi Mafita ga Talakawan Najeriya

Yar Majalisa Ta ce Ita ma Tana Jin Yunwa, Ta Fadi Mafita ga Talakawan Najeriya

  • Yayin da yan Najeriya ke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa da yunwa, yar majalisar tarayya, Adewunmi Onanuga ta yi magana
  • Hon. Adewunmi Onanuga ta ce halin wahala da ake ciki a Najeriya ba talakawa ne kawai suke fama ba, har da masu mulki da mukami
  • Haka zalika yar majalisar ta fadi shawarar da take ba mutanen mazabarta domin samun sauki kan halin da ake ciki na wahala a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yar majalisar tarayya, Hon. Adewunmi Onanuga ta yi kira ga yan Najeriya kan su koma noma domin yaki da yunwa.

Hon. Adewunmi Onanuga ta ce har su ma da suke rike da madafun iko suna fama da yunwa da wahalar rayuwa.

Kara karanta wannan

Mutumin Jonathan ya tono makircin da ake shiryawa Tinubu a Arewa bayan sayen jirgin sama

Onanuga
Yar majalisa ta bukaci talakawa su koma noma a Najeriya. Hoto: @adewunmionanuga
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yar majalisar ta buƙaci yan Najeriya su kara hakuri ga shugaba Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yar majalisa ta ce tana jin yunwa

Hon. Adewunmi Onanuga ta ce ita ma tana jin yunwa duk da cewa za a ga kamar ba alamar yunwa a tattare da ita.

Adewunmi Onanuga ta ce maimakon kuka a kan yunwa ya kamata mutane su canza tsarin gudanar da rayuwa.

Magana kan cire tallafin man fetur

Hon. Adewunmi Onanuga ta ce shugabannin da suka wuce sun gaza cire tallafin man fetur saboda suna tsoron a sauke su.

Yar majalisar ta ce dole za a yi hakuri ga shugaba Bola Tinubu domin gyara zai dauki lokaci kafin ya kammala.

"A koma noma" - 'Yar majalisa

Hon. Adewunmi Onanuga ta ce tana ba mutane shawarar komawa noma domin magance wahalar rayuwa da ake ciki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Lamari ya girma: Amnesty Int’l ta shiga dambarwar yan kwadago da yan sanda

Ta kara da cewa ko da a filin da yake bayan gidajen mutane ne za a iya fara noma domin neman sauƙin rayuwa.

Yan majalisa sun gargadi yan sanda

A wani rahoton, kun ji cewa yan majalisa daga jam'iyyun adawa sun caccaki matakin rundunar yan sandan kasar nan na gayyatar shugaban NLC, Joe Ajaero.

Rundunar ta mika takardar gayyata ga shugaban NLC, Joe Ajaero bisa zargin daukar nauyin ta'addanci yayin zanga-zanga a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng