An Gano Abin da Gwamnatin Tinubu Ke Boyewa kan Tallafin Man Fetur

An Gano Abin da Gwamnatin Tinubu Ke Boyewa kan Tallafin Man Fetur

  • Gwamnatin tarayya ta jawo cece-kuce kan kuɗaɗen da ta ce ta kashe wajen ganin jama'a sun sayi man fetur da arha
  • Wani mai kare haƙƙin jama'a ya yi bayanin cewa kuɗaɗen da gwamnatin ta biya ba tallafin man fetur ba ne domin ta daɗe da cire shi
  • Ibrahim Garba Wala ya bayyana cewa giɓin da ake samu idan farashin dala ya tashi ne ko farashin gangar mai gwamnatin ke biya amma ba tallafi ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta biyan kusan naira tiriliyan 7 a matsayin tallafin man fetur domin ganin jama'a basu sayi man da tsada ba.

A cewar gwamnatin ƙoƙarin da ta yi wajen zuba maƙuden kuɗaɗen su ne suka taimaka wajen hana hauhawar farashin man fetur ta yadda har ta kai ana iya sayen man da sauƙi a yanzu.

Kara karanta wannan

Matatar Ɗangote: Gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakin sauke farashin fetur a Najeriya

Bayani kan tallafin man fetur
Gwamnatin Tinubu ba ta biyan tallafin man fetur Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bayanin da gwamnatin ta yi ya jawo suka sosai saboda gwamnatin ta daɗe tana cewa ta cire tallafin man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tashar RFI Hausa ta yi hira da wani mai fafutukar kare haƙƙin jama'a, Ibrahim Garba Wala kan lamarin.

Tallafin man fetur ne ko kuwa?

IG Wala ya yi bayanin cewa kuɗaɗen da gwamnatin tarayyar ta biya ba tallafin man fetur ba ne domin ta daɗe da cire shi.

A cewarsa abin da gwamnatin tarayyar ke biya giɓi ne na bambancin da ake samu idan dala ta tashi ko farashin gangar mai ya tashi.

Ibrahim Garba Wala ya bayyana cewa ruɗanin da aka samu ya biyo bayan rashin fitowa da gwamnati ba ta yi ba, ta yi bayani kan haƙiƙanin abin da take biya.

"Ba tallafi Tinubu ke biya ba", I G Wala

Kara karanta wannan

Kisan kiyashi: Yadda maƙabartun Gaza suka cika ana birne gawa kan gawa

"Ba za mu yarda a kira shi tallafi ba, saboda a doka a hukumance gwamnati tana da daman a sassauta ko kuma a yiwa al'umma tallafi wanda doka ya ba da, kuma shi ne suka ce sun cire."
"Amma yanzu idan aka yi amfani da wannan kalmar a doka cewa tallafi ne, ba tallafi ba ne saboda an cire shi. Sai dai su tafi can saboda gazawa irin ta su wajen gudanar da tattalin arziƙi su san wane suna za su ba shi."
"Domin idan muka yarda cewa wannan tallafi ne, to doka ba ta san da shi ba, saboda sun riga da sun cire shi."

- Ibrahim Garba Wala

An buƙaci Tinubu ya kori minista

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin evangelical, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kori ministan wasanni, John Enoh.

Kara karanta wannan

Shekarau ya bayyana wani babban sirrinsa kafin ya zama gwamnan Kano

Primate Ayodele ya kafa hujja da rashin tabuka abin kirki da tawagar Najeriya ta yi a gasar Olympics da aka yi a birnin Paris na kasar Faransa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng