NDLEA Ta Kare Shirinta na Gwajin Kwaya ga Dalibai, Za a Dauki Mataki kan Wasu
- Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) za ta rika yi wa dalibai masu neman shiga manyan makarantu gwaji
- Ana sa ran gwajin zai taimaka wajen gano dalibai masu ta'ammali da miyagun kwayoyi da kuma taimaka masu da wasu dabaru
- Kwamandan NDLEA na Katsina, Hassan Sani Abubakar ya shaidawa Legit cewa dama shiri ne da ake yi, kuma zai kakkabe shaye-shaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce kar dalibai su ji tsoron shirinta na gwajin kwaya idan za a fara sabon zangon karatu.
Daraktan yada labaran hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana haka, inda ya ce ba ana yin shirin da zummar korar daliban da ake da tabbacin su na mu'amala da kwaya ba ne.
Jaridar Punch ta wallafa cewa an bijiro da shirin ne domin taimakawa matasan kasar nan da su ka tsunduma ta'ammali da miyagun kwayoyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Babafemi ya kara da cewa idan an samu masu ta'ammali da kwaya, akan taimaka masu da dabaru da sauran abubuwan da ake bukata domin rabuwa da halayyar.
"Gwajin kwaya na taimakawa," NDLEA
Shugaban hukumar hana sha da fataucin kwaya (NDLEA) reshen jihar Katsina, Hassan Sani Abubakar ya shaidawa Legit cewa dama an dade ana shirin.
Shugaban ya ce sun dade su na taimakon dalibai, musamman wadanda aka gano su na ta'ammali da miyagun kwayoyi har sai sun rabu da dabi'ar baki dayanta.
Ya shawarci hukumomin sauran manyan makarantu da su rika tuntubar hukumomin NDLEA a jihohinsu, domin akwai kayan aikin gwajin da zai wadata.
NDLEA ta kama masu ta'ammali da kwaya
A baya mun ruwaito cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Kano ta damke matasa maza da mata da ake zargi da ta'ammali da kwayoyi.
Hukumar ta ce a cikin watanni uku kacal, ta kama matasa 319 a sassa daban-daban, sannan an kama tan 4.7 na migayun kwayoyi daga wadanda aka kama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng