Jigawa: Mutanen da Suka Mutu a Ambaliyar Ruwa Sun Kai 28, Gwamna Ya Jero Dalilai
- Gwamna Umar Namadi ya tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasu sanadin ambaliyar ruwa ya kai 28 a jihar Jigawa
- Umar Namadi ya bayyana cewa galibin waɗanda suka rasa ransu ginin ƙasa ne ya rufta kansu da daddare a lokacin ambaliyar
- Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya karɓi bakuncin kwamitin kula da mahalli na majalisar wakilai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya ce adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a wasu sassan jihar ya kai 28.
Tun farko dai rahotanni sun nuna mutane 16 ne suka rasu yayin da fiye da 3000 suka rasa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 10 na Jigawa.
Da yake ƙarin haske kan ibtila'in ambaliyar wanda ya faru sakamakon mamakon ruwan sama, Gwamna Namadi ya ce adadin waɗanda suka rasu ya kai 28 a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya faɗi dalilin rasa rayuka
Ɗanmodi ya ƙara da cewa mafi akasarin waɗanda suka mutu gidajen ƙasa ne suka rufta kansu alokacin ambaliyar ruwan, Premium Times ta rahoto.
Gwamnan ya ce zuwa ranar Talata, ibtila'in ambaliyar ya taɓa magidanta 80,000 a ƙananan hukumomi 14.
Umar Namadi ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin majalisar wakilai mai kula da muhalli, karkashin jagorancin shugaba, Aminu Jaji.
Ƴan majalisar sun kai ziyara jihar Jigawa ne domin tantance irin ɓarnar da ambaliyar ruwan ta yiwa al'umma, rahoton Tribune Nigeria.
Ambaliya ta rusa gidaje a Jigawa
Gwamnan ya ce sama da gidaje 7,000 ne suka ruguje, sannan kuma ruwa ya shafe gonaki 6,500 a garuruwan da suka haura 135.
Namadi ya yi gargadin cewa za a iya samun karin barna nan gaba ganin yadda madatsun ruwa a jihar suka cika maƙil, kuma ba a saki ruwan da ke dam din Tiga ba.
Gwamnan ya ce jihar ba ta yi tsammanin ambaliyar ruwa a watan Agusta ba amma ayyukan titunan gwamnatin tarayya wanda ya toshe hanyoyin ruwa ne ya jawo matsalar.
Gwamna Namadi ya raba tallafin Tinubu
A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da fara rabon tallafin buhunan shinkafa, masara, dawa da gero ga masu ƙaramin ƙarfi a Jigawa.
Umar Namadi ya bayyana cewa za a raba tallafin a dukkan gundumomi 187 da ke ƙananan hukumomi 27 a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng