Badakalar Kwangila: Hukumar PCACC Ta Samu Nasara a Binciken da Take Yi
- PCACC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Kano ta samu umarnin rufe wani asusu a binciken da take yi kan badaƙalar kwangiloli
- Hukumar ta rufe asusun wanda yake ɗauke da N160m yayin da take ci gaba da yunƙurin ƙwato N440m na badaƙalar kwangilar
- Ɗan uwan Rabiu Kwankwaso da ake zargi da hannun kamfaninsa a badaƙalar, zai amsa tambayoyi wajen masu bincike ranar Alhamis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta samu umarnin rufe wani asusu a binciken da take kan badaƙalar kwangilar siyo magunguna a jihar.
Hukumar PCACC ta samu umarni rufe asusun mai ɗauke da N160m yayin da ta yi yunƙurin ƙwato N440m.
Ɗan uwan kwankwaso zai amsa tambayoyin PCACC
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran masu binciken hukumar za su ci gaba da yin tambayoyi ga wasu muhimman mutane da ake bincika, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma tattaro cewa, Musa Garba Kwankwaso, ɗan uwa ga jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso, zai fuskanci tambayoyi daga masu bincike a ranar Alhamis.
Ana sa ran zai amsa tambayoyi dangane da rawar da kamfaninsa, Novomed Pharmaceuticals ya taka a cikin badaƙalar kwangilar.
Hukumar PCACC ta gayyaci waɗanda ake zargi
A wata tattaunawa ta musamman da jaridar ta yi da shugaban hukumar PCACC, Muhuyi Magaji ya ce sun miƙa takardar gayyata ga waɗanda ake zargi da hannu a badaƙalar.
“Mun riga mun miƙa takardar gayyata ga mutane kusan biyar ko shida, ciki har da babban sakataren ma’aikatar ƙananan hukumomi da daraktan tsare-tsare."
- Muhuyi Magaji
Ya ce hukumar ta kuma gayyaci shugaban ƙungiyar kananan hukumomin Najeriya ALGON na jihar Kano da sakataren ƙungiyar na jiha da kakakin ƙungiyar na jiha.
PCACC ta fara bincike a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano (PCACC) ta fara gudanar da bincike kan tallafin abinci da shugaba Bola Tinubu ya turo da badakalar magani a jihar.
Hukumar na zargin ɗan uwan Rabi'u Kwankwaso ne mai suna Musa Garba Kwankwaso da shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Shehu Wada Sagagi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng