N90bn: EFCC Ta Fadi Yadda Aka Yi Binciken Sirri Wajen Bankado Badakalar NAHCON

N90bn: EFCC Ta Fadi Yadda Aka Yi Binciken Sirri Wajen Bankado Badakalar NAHCON

  • Hukumar yaki da masu yiw a tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana yadda aka gano badakala a NAHCON
  • EFCC na zargin tsohon shugaban NAHCON, Jalal Arabi da wasu manyan jami'ai da ruf da ciki kan tallafi N90bn da aka ba mahajjata
  • Hukumar ta ce akwai jami'inta na sirri da wasu da suka rika bincike a hukumar alhazai ta NAHCON har aka gano badakalar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta bayyana yadda aka yi aikin hadin gwiwa wajen gano badakala a hukumar alhazai.

Kara karanta wannan

Ba sani ba sabo: Gwamnatin Abba ta dura kan dan uwan Kwankwaso domin bincike

EFCC na zargin tsohon shugaban hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) ya hada baki da wasu kusoshin hukumar wajen wawure tallafin alhazan N90bn.

Hukumar EFCC
EFC ya ce jami'inta da fusatattun ma'aikata ne su ka fallasa badakalar N90bn a hukumar Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa wani jami'in EFCC da aka dasa a hukumar ya himmatu kwarai wajen samo bayanai a kan badakalar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma an samu wasu jami'an hukumar da ba su gamsu da yadda tsohon shugaban, Jalal Arabi da sakataren hukumar, Abdullahi Kotangora ke aiki ba.

Tun 2022 EFCC ke binciken NAHCON

Jaridar Punch ta wallafa cewa tun a shekarar 2022 hukumar EFCC ke binciken zargin badakala a hukumar NAHCON.

Zuwa yanzu, EFCC ta yi nasarar kwato kudin Saudiyya SR314,098 daga Jalal Arabi bayan an gano ya biya kansa da sauran jami'an hukumar fiye da kima.

NAHCON: EFCC ta gano kudin jami'ai

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisa ya kai agajin ambaliya a Yobe, ya tallafawa jama'a da miliyoyi

A ka'ida, shugaban hukumar zai samu SR15,929, amma ya biya kansa SR50,000; binciken ya gano kwamishinoni uku da ya kamata a biya SR15,929, amma kowannensu ya samu SR 40,000.

Shi ma sakataren hukumar, Abdullahi Kotangora ya samu SR30,000 a maimakon SR14,336, sai daraktoci da shugaban ma'aikata da aka biya SR30,000 maimakon SR2,550.

EFCC ta tsare shugaban hukumar NAHCON

A wani labarin kun ji cewa hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC), ta tsare tsohon shugaban hukumar kula da aikin hajji ta kasa, Jalal Arabi.

Hukumar EFCC na zargin Jalal Arabi da wasu kusoshin hukumar NAHCON da badakalar tallafin N90bn da shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba wa mahajjata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.