Matasa Sun Kwaci Yan Fashi a Hannun Yan Sanda, Sun Cinnawa 1 Wuta

Matasa Sun Kwaci Yan Fashi a Hannun Yan Sanda, Sun Cinnawa 1 Wuta

  • Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta bayyana yadda wasu matasa suka kwace wanda ake zargi sun yi sata suka kashe su
  • Kakakin yan sanda a jihar Bauchi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Misau zuwa Kari a karamar hukumar Misau
  • Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi ya yi kira ga matasa kan daukan doka a hannu tare da fadan matakin da za su dauka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda Najeriya a Bauchi ta bayyana yadda wasu matasa suka kashe waɗanda ake zargi da kisan kai.

Kakakin rundunar a jihar Bauchi, Ahmed Wakili ya tabbatar da kashe mutanen a kan hanyar Misau zuwa Kari.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, yan gida daya su 5 sun mutu daga shan miyar gishirin lalle

Bauchi
Matasa sun kashe mutanen da ake zargi da kisan kai a Bauchi. Hoto: Nigerian Police Force Bauchi State Command
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa kwamishinan yan sanda a jihar Bauchi ya yi kira na musamman ga matasa bayan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asalin abin da ya faru a Misau

Yan sanda sun bayyana cewa a ranar 18 ga Agusta suka samu rahoto kan an samu wata gawa kwance cikin jini a unguwar Agwaluma a Misau.

Biyo bayan haka, yan sanda suka tura runduna ta musamman domin duba hakikanin abin da ya faru a wajen da aka samu gawar.

Bayan bincike an gano cewa wani mutum mai suna Muhammad Mamuda Baba ne da ke sana'ar acaɓa aka kashe aka dauke masa babur.

Matasa sun kashe mutane biyu a Misau

Rahoton Channels Television ya nuna cewa a ranar 19 ga watan Agusta yan sanda suka kama mutane biyu a kan babur din da aka kashe mai acaɓa suna ƙoƙarin guduwa.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sandan Kano ta kadu da karuwar asarar rayuka, an gano dalilai

Ana cikin haka matasa suka nuna yawa ga yan sanda suka kwace mutanen daga wajen yan sanda suka kunna wuta ga daya, dayan kuma suka kashe shi.

Kwamishinan yan sanda a jihar Bauchi, Auwal Muhammad ya yi kira ga matasa a kan su kaucewa daukar doka a hannu ya kuma ce za a binciki waɗanda aka kama da laifi.

An kashe mutane a Benue

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mahara a kan babura sun farmaki kauyen Gugur a karamar hukumar Katsina Ala da ke jihar Binuwai.

Wakilin yankin a majalisar jiha, Jonathan Agbidye ya tabbatar da harin sai dai ya ce harin na ramuwar gayya ne, kuma yanzu kura ta lafa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng