Shari'ar EFCC: Kotu Ta Lalata Shirin Yahaya Bello, Ta Bukaci Ya Gurfana Gabanta

Shari'ar EFCC: Kotu Ta Lalata Shirin Yahaya Bello, Ta Bukaci Ya Gurfana Gabanta

Abuja - Rahoton da muke samu yanzu na nuni da cewa kotun daukaka ta ba da sabon hukunci kan shari'ar da ake yi tsakanin EFCC da Yahaya Bello.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

An ce kotun ta umarci tsohon gwamnan na jihar Kogi da ya mika kansa domin gurfana gabanta kan tuhume-tuhumen da hukumar EFCC ke yi masa.

Gidan talabijin na TVC News ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a yammacin ranar Talata, 20 ga watan Agustan 2024.

A cewar rahoton, kotun ta kuma hana Yahaya Bello daukar wasu matakai na tuhume-tuhumen har sai dai idan an gurfanar da shi a gaban kuliyar.

Yanzu dai kotun ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun jihar Kogi ta yanke.

Kara karanta wannan

Novomed: Shugaban APC a kano ya nemi EFCC ta binciki kwangilar magunguna

Duba rahoton a kasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikakken labarin na zuwa...

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.