Maido Tallafin Mai: Kamar Atiku, An Zargi NNPCL da Rashin Fito da Bayanai Filla Filla
- Tsohon sakataren gudanarwan kungiyar NEITI, Waziri Adio ya bukaci kamfanin NNPCL ya fito fili ya yi bayani dalla dalla kan tallafin mai
- Waziri Adio ya ce akwai lauje cikin nadi kan yadda NNPCL yake kauce-kauce wajen bayanin maido da tallafin man fetur a Najeriya
- Hakan na zuwa ne bayan kamfanin NNPCL ya musanta zancen cewa ya dawo da biyan tallafin man fetur bayan umarnin Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kamfanin NNPCL na cigaba da shan suka kan karin bayani da ya yi a kan dawo da tallafin man fetur.
Tsohon shugaban hukumar NEITI, Waziri Adio ya shiga sahun masu sukar NNPCL kan maganar tallafin man fetur.
Legit ta tatttaro bayanan da Waziri Adio ya yi kan tallafin man fetur ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tallafin mai: Maganar da NNPCL ya yi
Kamfanin NNPCL ya yi martani kan cewa bai dawo da tallafi man fetur ba kamar yadda aka rika yaɗawa a kafafen sadarwa.
Legit ta ruwaito cewa NNPCL ya ce yana rage kudin da ya shigo da mai ne ga gwamnatin tarayya ba yana ba yan kasuwa kudin tallafi ba ne.
Adio ya bukaci karin haske daga NNPCL
Daily Trust ta wallafa cewa Waziri Adio ya ce maganar da NNPCL ya yi ba ta gamsar da yan kasa ba kan kudin da ake kashewa.
Saboda haka ya ce akwai bukatar NNPCL ya fito fili ya yi bayani dalla dalla a kan halin da ake ciki kan kudin da gwamnati ke kashewa da sunan tallafi.
Maganar rage kudin mai ga gwamnati
Waziri Adio ya ce maganar rage kudin mai ga gwamnatin tarayya kwata kwata ba ta taso ba kuma fadin hakan wasa da hankalin yan Najeriya ne.
Ya kara da cewa shawarar da zai ba NNPCL kawai ita ce ya daina tono matsaloli, ya yi bayani kan hakikanin abin da yake faruwa.
Atiku ya yi magana kan tallafin mai
A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar ya soki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan ci gaba da biyan tallafin man fetur a Najeriya.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce bayanan da ke fitowa sun ƙara nuna akwai tufka da warwara da shakku a gwamnati mai ci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng