Malamin Musulunci Ya Tsoma Baki, Ya Haskawa Gwamna Hanyar Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga

Malamin Musulunci Ya Tsoma Baki, Ya Haskawa Gwamna Hanyar Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga

  • Sheikh Abdulrahaman Azzamfari ya koka kan halin matsin da miyagun ƴan bindiga suka ƙara jefa mutane a jihar Zamfara
  • Malamin addinin ya ce gwamnatin Dauda Lawal ta yi sanyi domin ta gaza shawo kan babban abin da ya fi takurawa al'umma
  • Shehin ya ce ya zama wajibi gwamnati ta rungumi hanyar sulhu domin ɗaukar matakin soji kaɗai ba zai warware matsalar ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Wani malamin addinin Islama, Sheikh Abdulrahaman Azzamfari, ya fsoma baki kan matsalar ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Sheikh Abdulrahaman ya aikawa Gwamna Dauda Lawal da saƙo, inda ya nuna damuwa game da yadda ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka a jihar.

Kara karanta wannan

Daga karin kumallo, uwa da ƴaƴanta 3 sun rasu a wani yanayi mai ban tausayi

Gwamna Dauda Lawal.
Sheikh Abdulrahaman ya koka kan halin da ƴan bindiga suke jefa mutane a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Malamin ya ce gwamnati mai ci karkashin Dauda Lawal ta gaza lalubo mafita, wanda hakan ya bai wa ƴan bindiga damar ci gaba da kai hare-hare kan jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa malamin ya yi kira ga gwamnatin Zamfara ta tashi tsaye domin daƙile matsalar tsaron da a yanzu take ƙara ta'azzara.

Malamin ya aika sako ga Gwamna Lawal

"Ya kamata gwamnatin Zamfara ta san mummunan halin da muke ciki, mutane na da gonaki amma ba su iya zuwa balle su noma wani abu da zai amfane su.
"Lamarin ya yi muni, ga yunwa da tsadar rayuwa wanda ke tilastawa mutane su bar gidanjensu da gonakinsu, wasu ma zuwa suke su shiga aikata miyagun laifuka.
"Amfani da karfin soji kaɗai ba zai warware matsalar nan ba, ya kamata a zauna a tattauna kuma a yi sulhu da waɗanda lamarin da shafa.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi zazzafan martani ga Shugaba Tinubu kan dawo da tallafin man fetur

Sheikh Abdulraham ya bukaci a yi sulhu

Shehin malamin ya ce ya zama wajibi gwamnatin Dauda Lawal ta bi hanyar sulhu domin matsalar tsaro ta zarce duk inda ake tunani a jihar Zamfara.

"Dole ne gwamnatin jihar Zamfara ta dauki matakai na sulhu, saboda lamarin ya wuce tunani kuma akwai bukatar a haɗa kai wuri ɗaya don kawo karshen lamarin."

Sojoji sun murƙushe ƴan bindiga

A wani labarin kuma sojojin Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri na miyagun ƴan bindiga a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma.

Sojojin na rundunar Operation Hadarin Daji sun yi nasarar sheƙe ƴan bindiga mutum biyu bayan sun yi musayar wuta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262