Abubuwan Sani kan Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayin da Ya Cika Shekara 83

Abubuwan Sani kan Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayin da Ya Cika Shekara 83

Jihar Minna - A ranar 17 ga watan Agustan 2024, tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya cika shekara 83 a duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Tsohon shugaban ƙasan yana daga cikin mutanen da idan aka zo ba da tarihin Najeriya, ba zai cika ba sai an ambato sunansa.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya cika shekara 83
Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya mulki Najeriya har na tsawon shekara takwas Hoto: @Searchmediamx
Asali: Twitter

Abubuwan sani kan Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Legit Hausa ta yi duba kan muhimman abubuwan da ya kamata a sani kan tsohon shugaban ƙasan na mulkin soja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tarihin Ibrahim Badamasi Babangida

An haifi Janar Ibrahim Badamasi Babangida a ranar 17 ga watan Agustan 1941 a garin Minna da ke jihar Neja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace kwamishina da matarsa a hanyar zuwa ɗaura auren ɗiyar gwamna

Ya yi karatunsa na firamare daga shekarar 1950 zuwa 1956. Daga shekarar 1957 zuwa 1962 ya yi karatu a makarantar sakandire ta gwamnatin tarayya da ke Bida a jihar Neja.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya shiga aikin soja a ranar, 10 ga watan Disamba 1962 inda ya halarci makarantar horar da sojoji da ke Kaduna.

Zamansa a aikin soja

Janar Ibrahim Badamasi Babangida yana ɗaya daga cikin sojojin da ake alfahari da su saboda juriyarsa da rashin tsoro, cewar rahoton Kalahari Review.

A lokacin da ya kwashe yana aikin soja, ya riƙa samun ƙarin girma har zuwa matakin Janar.

Yana daga cikin kwamandojin da suka jagoranci yaƙin basasa da aka yi a Najeriya da ƴan awaren Biafra. A lokacin yaƙin ne aka yi masa wani harbi wanda har yanzu yana ɗauke da ɓurɓushin harsashin a jikinsa.

A lokacin da yake aikin soja, ya shiga cikin dukkanin juyin mulkin da aka yi a ƙasar nan ban da guda biyu. Na farkon shi ne wanda aka yi a shekarar 1966, sai na biyun wanda Laftanal Kanal Dimka ya jagoranta a shekarar 1976.

Kara karanta wannan

Sabon ɗan Majalisar PDP da aka rantsar ya yi magana kan yiwuwar sauya sheka

Zaman Janar IBB shugaban ƙasa

A ranar 27 ga watan Agustan 1985, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya zama shugaban ƙasa bayan ya kifar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi mulkin Najeriya har na tsawon shekara takwas.

A lokacin mulkinsa ya gudanar da muhimman ayyukan raya ƙasa da kafa hukumomin gwamnatin tarayya ciki har da hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC).

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ƙirƙiro jihohi guda 11 a lokacin mulkinsa.

A lokacin mulkinsa ne kuma ya soke zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1992, wanda ake tunanin MKO Abiola ya lashe.

Siyasar Janar IBB

Janar Ibrahim Badamasi ya taka rawa wajen komawar Najeriya kan tsarin mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1998.

Janar IBB yana daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar PDP tare da irin su Janar Aliyu Mohammed Gusau.

A shekarar 2006, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP. Sai dai daga baya ya janye daga yin takarar.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya ragargaji Abba kan 'sakacin' sace takardun shari'ar Ganduje

A shekarar 2010 ya sake nuna aniyarsa ta yin takarar shugaban ƙasa, sai dai daga baya ya sake janyewa.

Iyalan Ibrahim Badamasi Babangida

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya auri Maryam Babangida a shekarar 1969 har zuwa lokacin da ta rasu a shekarar 2009.

Suna da ƴaƴa huɗu da suka haɗa da Aisha, Muhammad, Aminu da Halima.

Janar IBB ya faɗi hanyar gyara Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja a Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bukaci dawo da darussan addini a makarantu.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana cewa sai an dawo koyawa dalibai addinansu a makarantu kafin a samu canjin da ake buƙata a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng