Tsohon Shugaban Majalisa Ya Kai Agajin Ambaliya a Yobe, Ya Tallafawa Jama'a da Miliyoyi

Tsohon Shugaban Majalisa Ya Kai Agajin Ambaliya a Yobe, Ya Tallafawa Jama'a da Miliyoyi

  • Mazauna Yobe sun shiga sahun wadanda ambaliya ta daidaita daga wasu gidajensu a wasu yankunan jihar
  • Jama'ar da ke Yobe ta Arewa su na daga cikin mazauna jihar da ambaliya ya yiwa mummunan ta'adi tare da raba wasu da gidajensu
  • Tsohon shugaban majalisa da ke wakiltarsu a majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya kai masu gudunmawar Naira Miliyan 25

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe - Tsohon shugaban majalisa, Ahmad Lawan ya kai wa jama'ar da ya ke wakilta na Yobe ta Arewa dauki bayan ambaliyar ruwa ya raba su da gidajensu.

Rt. Hon Ahmad Lawan ya mika tallafin Naira Miliyan 25 a karshen mako yayin ziyarar jaje ga kananan hukumomin Karasuwa da Nguru da ambaliya ta yi kamari.

Kara karanta wannan

Murna za ta koma ciki? Ambaliya ta fara barazana ga wadatar abinci

Sanata
Tsohon shugaban majalisa ya kai tallafin N25M mazabarsa Hoto: Ahmad Ibrahim Lawan
Asali: Facebook

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanatan ya bayar da Naira Miliyan 20 ga wadanda iftila'in ya rutsa da su a karamar hukumar Nguru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da na Karasuwa su ka samu Naira Miliyan 5 saboda su da sauki idan aka kwatanta da yankin Nguru a jihar.

Ambaliya: Sanata ya nemi tallafawa jama'a

Dr. Hon. Ahmad Lawan ya nemi hukumar bayar da agaji ta kasa (NEMA) da ta jiha da su tabbata an magance matsalolin mutanen da ambaliya ya rutsa da su.

Jaridar The Nation ta wallafa cewa Sanatan ya yaba da kokarin hukumomin, amma ya ce akwai bukatar a rubanya kokari ganin irin halin da mutanen ke ciki.

Sanata Ahmad Lawan ya shawarci wadanda iftila'in ya shafa su bayar da hadin kai ta hanyar bin umarnin hukumomin agajin domin tsare lafiyarsu da tallafa masu.

Kara karanta wannan

Yunwa: Marayu 5 da mahaifiyarsu sun kwanta dama a Kano

Ana fargabar ballewar ambaliya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kaduna ta ce akwai fargabar za a samu ambaliya a kananan hukumomi bakwai da ke jihar.

Hukumar agajin ta shawarci mazauna yankunan su gaggauta barin wuraren domin tsira da rayuwarsu daga ambaliyar da ake sa ran zai afku ko yaushe daga yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.