Abba Ya Fara Canza Fasalin Birnin Kano, Ya Dauko Tsarin Kasashen Waje
- Gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta dauki haramar gina birane kamar yadda ake yi a wasu ƙasashe
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara ƙoƙarin biyan kudi ga wadanda za a yi amfani da filayensu wajen gina biranen
- Gwamnatin Kano ta bayyana cewa za a gina biranen ne domin a samar da wuraren da wasu za su koma domin rage cinkoso
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Abba Kabir Yusuf ya fara yunkurin samar da birane a Kano ta inda zai gina gidajen zamani a nesa da gari.
Gwamnatin ta fara shirin biyan kudi ga mutanen da za a yi amfani da filayensu wadanda galibinsu manoma ne.
Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ina za a gina biranen a Kano?
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa za a gina birni na farko ne a kauyukan Yargaya da Gwangwan a karamar hukumar Dawakin Kudu.
Haka zalika gwamnatin ta tabbatar da cewa za a gina wani birni a Unguwar Rimi da Lambu da ke karamar hukumar Tofa.
Dalili samar da birane a Kano
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa za a samar da biranen ne domin rage cinkoso da kuma raya birane a jihar Kano.
Ya kuma kara da cewa samar da biranen zai farfaɗo da tattalin jihar da inganta rayuwar al'ummar yankin.
Za a biya mutane kudin filaye
Gwamnatin Kano ta fara shirin biyan mutanen da aikin zai shafi filaye da gonakinsu kudi inda gwamna ya gana da su.
Abba Kabir ya yi kira na musamman ga mutanen yankunan da su karbi aikin hannu biyu biyu domin an yi shi ne kan inganta yankunansu.
Yan NNPP sun sauya sheka a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa yan siyasa a jihar Kano na cigaba da sauya sheka daga jam'iyyun siyasa daban daban tun kafin fara maganar zaben 2027.
Wasu daga cikin manya a tafiyar jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai adawa a jihar Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng