Yan Sanda Sun Gayyaci Shugaban NLC Kan Zargin Ɗaukar Nauyin Ta'addanci, Bayanai Sun Fito
- Rundunar ƴan sanda ta gayyaci shugaban kungiyar kwadago NLC, Kwamared Joe Ajaero kan zargin hannu a ayyukan ta'addanci
- A wata sanarwa da ta fito daga sashen leken asiri na rundunar, ta buƙaci Ajaero ya kai kansa ranar Talata da misalin karfe 10:00 na safe
- Wannan dai na zuwa ne bayan samamen da ƴan sanda suka kai hedkwatar NLC da ke babban birnin tarayya Abuja kwanakin baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gayyaci Joe Ajaero, shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC domin amsa wasu tambayoyi.
Ƴan sandan sun gayyaci shugaban NLC na ƙasa kan zargin hannu a ɗaukar nauyin ayyukan ta'addanci, laifukan intanet da wasu zarge-zarge.
Hakan na kunshe ne a wata takarda da aka wallafa a manhajar X da ta fito daga ofishin mataimakin kwamishinan ƴan sanda na sashin leƙen asiri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun yi barazanar kama Ajaero
Takardar mai dauke da sa hannun Adamu S. Muazu ta yi barazanar cewa idan Ajaero ya yi kunnen ƙashi, ya ƙi mutunta gayyatar, ƴan sanda na iya kama shi.
Wani sashin takardar ya ce:
"Wannan ofishin na gudanar da bincike kan haɗa baki wajen aikata mugayen laifuka, ɗaukar nauyin ta'addanci, cin amanar ƙasa da laifukan intanet wanda ka faɗo ciki.
"Don haka ana bukatar ka zo ka amsa tambayoyi ranar Talata, 20 ga watan Agusta, 2024 da misalin karfe 10:00 na safe a Abuja."
NLC na zargin gwamnatin tarayya
A ƴan kwanakin nan NLC ta zargi gwamnati da yiwa kungiyar bita da ƙulli bayan wani samame da jami'an tsaro suka kai a hedikwatar NLC da ke Abuja.
Rundunar ƴan sanda ta fito ta bayyana cewa ta kai samame hedkwatar NLC da nufin kama wani ɗan ta'adda da ya shigo ƙasar nan da nufin tayar da tarzoma a lokacin zanga-zanga.
Sai dai NLC ta yi fatali wannan uzuri na ƴan sanda, inda ƙungiyar kwaɗagon ta ce duk kame-kame ne domin kare kai.
Bayan wannan musayar yawu ne a yanzu ƴan sanda suka gayyaci shugaban NLC bisa zargin hannu a aikata manyan laifuka.
Matawalle ya yi magana kan makamai
A wani rahoton kuma karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa jami'an tsaron kasar nan na bukatar alburusai da dama domin yakar ta'addanci.
Ministan ya ce ana bukatar akalla alburusai miliyan 350 domin rabawa dakarun sojoji, 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a kowace shekara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng