"Sanarwa ce": ASUU Ta Shaida Shirin Tsunduma Yajin Aiki a Dukkanin Jami’o’in Najeriya

"Sanarwa ce": ASUU Ta Shaida Shirin Tsunduma Yajin Aiki a Dukkanin Jami’o’in Najeriya

  • Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) ta aika sanarwa ga gwamnatin Bola Tinubu cewa za ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani
  • Kungiyar ASUU ta ce nan da kwanaki 21 masu zuwa za ta garkame dukkanin jami'o'in kasar, kuma ba ta bayyana ranar budewa ba
  • A cewar malaman jami'ar, wannan sanarwa ce ba wai gargadi ba, kuma ta yi hakan domin kiyaye dokokin shiga yajin aiki a kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ibadan - Kungiyar malaman jami’o’i ta sanar da gwamnatin tarayya shirin ta na shiga yajin aikin gama-gari a fadin kasar nan.

Kungiyar ASUU ta sanar da gwamnatin Bola Tinubu cewa nan da kwanaki 21 za ta garkame jami'o'in kasar, kuma wannan ba wa'adi ba ne.

Kara karanta wannan

Murna za ta koma ciki? Ambaliya ta fara barazana ga wadatar abinci

Kungiyar ASUU ta yi magana kan shiga yajin aiki a fadin Najeriya
Kungiyar ASUU ta sanya ranar shiga yajin aiki a fadin Najeriya. Hoto: @officialABAT, @asuunews
Asali: Twitter

Wasu majiyoyi daga majalisar zartarwar kungiyar ASUU ta kasa sun tabbatar wa da The Punch a Abuja wannan ci gaban a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ASUU ta sanar da shirin shiga yajin-aiki

An fitar da sanarwar ne a karshen taron majalisar NEC ta kungiyar da aka gudanar a jami’ar Ibadan, kuma ana sa ran mika kwafin ga ma’aikatun kwadago da ilimi na tarayya.

“Ba wa'adi ba ne, wannan sanarwa ce muka ba gwamnati. Mun ba ta sanarwar kwana 21 cewa za mu tsunduma yajin aiki idan kwanakin suka kare.
"Mun fitar da sanarwar ne domin cika sharudan dokokin kwadago, muna kokarin tabbatar da cewa duk ayyukanmu sun yi daidai da doka."

- A cewar majiyar.

Matsalolin da ASUU ke kokarin magancewa

Idan dai za a iya tunawa, mun ruwaito cewa ASUU ta yi barazanar shiga yajin aikin saboda rashin aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma da gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Miyagu sun nuna karfin hali, sun kashe jami'in gwamnati kusa da gida a Nasarawa

A ranar 26 ga watan Yuni ne ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya gayyaci kungiyar kwadagon zuwa wani taron tattaunawa kan batutuwan da suka shafi jami’o’i da kuma dakile yajin aikin da suka shirya yi.

Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke wanda ya yi magana kan sakamakon taron ya ce ba a aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla da gwamnatin tarayya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.