An yi Gumurzu tsakanin Sojoji da Yan Boko Haram, an Kashe Babban Ɗan Ta’adda

An yi Gumurzu tsakanin Sojoji da Yan Boko Haram, an Kashe Babban Ɗan Ta’adda

  • Rahotanni na nuni da cewa an yi gumurzu tsakanin rundunar sojin Najeriya da yan ta'addar Boko Haram a jihar Borno
  • Rundunar sojin ta bayyana cewa ta samu nasarar kashe babban ɗan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo yayin gumurzun
  • Haka zalika rundunar ta bayyana karin nasar da ta samu wajen kashe wasu yan ta'adda da yadda wasu suka mika wuya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Rundunar sojin Najeriya ta yi kazamin fada da wasu yan ta'addar Boko Haram a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin Najeriya ta kwato makamai da wasu abubuwa da yan ta'addar ke amfani da su.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, yan gida daya su 5 sun mutu daga shan miyar gishirin lalle

Sojojin Najeriya
Sojoji sun kashe yan Boko Haram. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Premium Times ta wallafa cewa cikin abubuwan da sojojin Najeriya suka kwato akwai miyagun kwayoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe babban ɗan Boko Haram

A ranar Asabar ne rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe babban ɗan Boko Haram da ake nema ido rufe.

Pulse Nigeria ta wallafa cewa rundunar sojin ta bayyana cewa ta yi musayar wuta ne da yan ta'addar kafin samun nasara a kansu.

Wasu yan Boko Haram sun mika wuya

Biyo bayan cin nasara da sojoji suka yi a kan yan Boko Haram, wasu yan ta'adda da iyalansu takwas sun mika wuya ga sojoji.

A cikin gumurzun da sojojin Najeriya suka yi da ƴan ta'addar an kashe yan ta'addar Boko Haram guda uku.

Kayan da aka kwato wajen Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta samu nasarar kwato bindiga kirar AK47 guda daya da wayoyin hannu da dama.

Kara karanta wannan

An gano abin da yarjejeniya tsakanin Najeriya da kasar Equatorial Guinea ta kunsa

Haka zalika rundunar ta tabbatar da kwato jakakkuna dauke da miyagun kwayoyi guda 52 wajen yan ta'addar.

Safarar makami: Sojoji sun cafke dan farauta

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun cafke wani shugaban ƙungiyar mafarauta a jihar Taraba.

Sojojin sun cafke Alhaji Adamu Tanko ne bisa zarginsa da siyar da bindiga ƙirar AK-47 ga wani da ake zargin cewa ɗan ta'adda ne da ke fitinar mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng