Novomed: Shugaban APC a Kano Ya Nemi EFCC Ta Binciki Kwangilar Magunguna
- Tun bayan da mai amfani da kafar sada zumunta, Dr. Bello Galadanci ya fitar da bidiyon zargin kwangila a Kano, ya bude kofar karin zargi
- A bidiyon, Dr. Galadanci da aka fi sani da dan Bello, ya yi zargin an hada baki da kananan hukumomi wajen ba wa kanin Rabiu Kwankwaso kwangila
- Tuni APC ta ce ba zai yiwu ba, har tayi kira ga hukumar EFCC ta tabbata ta bi diddigin duk wani lamari da ya shafi bayar da kwangilar maganin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Jam'iyyar APC reshen Kano ta nemi hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta binciki gwamnatin jihar bisa zargin kwangila.
A sanarwar da shugaban jam'iyya a Kano, Abdullahi Abbas ya fitar, ya ce akwai ayar tambaya kan zargin baya-bayan nan na ba kamfanin Novomed kwangilar miliyoyi.
"Abba bai shirya ba" Inji Kano APC
Nigerian Tribune ta wallafa cewa APC na ganin yadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ba shi da masaniya kan kwangilar, ya nuna bai shirya mulkin Kano ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Abdullahi Abbas ya ce sun dade su na zargin gwamnatin da zagwanye tattalin arzikin jihar, kuma lokaci ya yi da za a taka mata birki
APC ta nemi rufe asusun kananan hukumomi
Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya nemi hukumar EFCC ta rufe asusun kananan hukumomin Kano 44, Daily Post ta wallafa.
Ya ce wannan zai dakile ci gaba da almundahanar kananan hukumomin jihar da gwamnatin NNPP, karkashin Abba Kabir Yusuf ke yi.
Fitaccen mai amfani da shafukan sada zumunta, Dan Bello ne ya yi zargin kananan hukumomin sun yi bai daya wajen ba kamfanin Novomed - mallakin 'danuwan Sanata Rabiu Kwankwaso kwangila.
Ganduje zai iya rasa shugabancin APC
A wani labarin kun ji cewa zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yiwa shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje zai iya jawo masa asara.
Wasu rahotanni da APC ta karyata daga baya sun nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara yiwa Abdullahi Ganduje tayin jakadan kasar waje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng