Murna za Ta Koma Ciki? Ambaliya Ta Fara Barazana ga Wadatar Abinci a Jihohi 10

Murna za Ta Koma Ciki? Ambaliya Ta Fara Barazana ga Wadatar Abinci a Jihohi 10

  • Yayin da ake shan ruwa kamar da bakin kwarya a sassan Arewacin Najeriya, an fara fargabar illar da hakan zai yi ga manoma
  • Masu ruwa da tsaki a fannin noma sun nemi gwamnati ta gaggauta ayyana dokar ta ɓaci a fannin samawa kasa abinci
  • Ana fargabar ruwan zai lalata gonaki da sauran abincin da ba a girbe ba, wanda haka zai jawo dimbin asara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kwararru a bangaren noma sun fara kokawa kan yiwuwar samun karancin abinci matukar ambaliyar ruwa ta ci gaba a jihohin Arewa da aka sani da noma.

Kara karanta wannan

Damina mai albarka: An fara ganin saukin abinci a Kano, jihohin Arewa maso Yamma

Manoma sun fara girbin shuka da wuri,wanda hakan ya fara kawo saukin farashin kayan hatsi da na gwari a kasuwannin da ke yankin.

Ambaliya
Ana fargabar ambaliya za ta jawo karancin abinci Hoto: Shehu Iliyasu
Asali: Facebook

Jihohi a matsalar ambaliya

Jaridar Punch ta wallafa cewa jihohi Arewa, da su ka yi fice a fannin noma na fuskantar barazanar mummunar ambaliya, wanda hukumar hasashen yanayi ta yi gargadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohin sun hada da Kano, Jigawa, Nasarawa, Taraba, Bauchi, Zamfara, Yobe, Sokoto da Kebbi, inda a yanzu haka ana jera kwanaki ana ruwa a wasu daga ciki.

Yadda ambaliya ke lalata gonaki

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na Jigawa, Dr. Haruna Mairiga ya bayyana cewa zuwa yanzu ambaliya ya lalata gonaki kadada 2,744 a sassan jihar.

Ya ce ambaliyar ta yi barna a kananan hukumomi 12 a jihar, da su ka hada da Buji, Kafin Hausa, Auyo, Hadejia, Birniwa, Malam Madori, Garki, Taura, Gwaram, Dutse, Kiyawa da Jahun.

Kara karanta wannan

Yunwa: Marayu 5 da mahaifiyarsu sun kwanta dama a Kano

Dr. Haruna Mairiga ya ce alkaluma sun tabbatar masu da cewa akalla, manoma sun yi asarar N1bn zuwa yanzu.

Sabon abinci ya fara zuwa daga gonaki

A wani labarin kun ji cewa sabon abinci ya fara shiga wasu daga cikin kasuwannin da ke jihohi yankin Arewa maso Yamma.

Lamarin ya fara jawo saukar farashin kayan hatsi kamar masara, gero da dasa da kayan miya a wasu jihohin da su ka hada da Kano, Katsina da Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.