Bayanai Sun Fito kan Umurnin Tinubu na Maido Tallafi duk da Ana Sayen Fetur a N900

Bayanai Sun Fito kan Umurnin Tinubu na Maido Tallafi duk da Ana Sayen Fetur a N900

  • Rahotanni na nuni da cewa Bola Ahmed Tinubu ya umurci kamfanin NNPCL da dawo da biyan tallafin man fetur
  • Kamfanin NNPCL ya bayyana adadin makudan kudi da gwamnatin tarayya za ta kashe domin biyan tallafin mai din
  • An ruwaito cewa hakan na zuwa ne bayan kamfanin ya koka ga shugaban kasa kan matsalolin da yake fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni na nuni da cewa kamfanin NNPCL ya samu damar dawo da tallafin man fetur daga fadar shugaban kasa.

An ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ba kamfanin izini ne bayan ya koka kan rashin samun daidaito wajen shigo da mai.

Kara karanta wannan

An zargi Gwamnatin shugaba Tinubu da satar dabarar tattalin arziki a wajen Atiku

shugaba Tinubu
Tinubu ya yi maganar dawo da tallafin man fetur. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar the Cable ta ruwaito cewa kamfanin NNPCL zai daina shigar da wasu kudin haraji ga asusun gwamnatin tarayya domin samun damar biyan tallafin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cire tallafin man fetur a Najeriya

Tun ranar da aka rantsar da shugaban kasa Bola Tinubu ya furta cewa ya cire tallafin man fetur a Najeriya.

Haka zalika ya jaddada cewa cire tallafin mai ya zama dole a Najeriya a lokacin da yake jawabi kan masu zanga zangar tsadar rayuwa.

Maganar dawo da tallafin fetur

A yau Litinin jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya amicewa kamfanin NNPCL ya dawo da biyan tallafin man fetur.

A yanzu haka Bola Tinubu ya amincewa kamfanin ya yi amfani da wasu kudin haraji da ake turawa asusun gwamantin tarayya domin biyan kudin tallafin mai.

Nawa za a kashe kan tallafin mai?

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya tashi bayan kotun turai ta saka Najeriya a gaba kan jirage 3

Bincike ya nuna cewa daga watan Agustan 2023 zuwa Disambar 2024 za a kashe sama da Naira triliyan 6 domin biyan tallafin mai.

Sai dai har yanzu ba a samu bayanai kan adadin kudin da za a daina turawa ga gwamnatin tarayya domin biyan tallafin mai din ba.

Atiku ya yi maganar tallafin man fetur

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan yadda Bola Ahmed Tinubu ya ke jagorantar Najeriya.

Atiku Abubakar ya ce akwai lauje cikin naɗi kan yadda Bola Tinubu ya gaza yiwa ƴan kasa bayani kan lamarin dawo tallafin man fetur.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng