Bayan Saka Ranar Zanga Zanga ta 2, Tinubu Zai Gana da Matasa a Najeriya
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da matasan Najeriya har 3,000 domin tattaunawa kan kawo cigaba a fadin ƙasar kan
- Shugaban matasan jam'iyyar APC na kasa, Dayo Israel ne ya fitar da sanarwa kan yadda taron zai gudana a fadar shugaban kasa
- Hakan na zuwa ne bayan matasan Najeriya sun fitar da sanarwar sake zanga zangar tsadar rayuwa a ranar 1 ga watan Oktoba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron matasa da zai gudana a fadar shugaban kasa.
Haka zalika mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima na cikin waɗanda za su halarci taron manyan goben.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa shugaban matasan APC na kasa, Dayo Israel ne ya bayyana yadda taron zai gudana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalili taron matasan Najeriya na 2024
Shugaban matasan APC na kasa, Dayo Israel ya bayyana cewa sun shirya taron ne domin ba matasa 3,000 damar cin gajiyar tsare tsaren Bola Tinubu.
Haka zalika Dayo Israel ya kara da cewa taron zai mayar da hankali kan samar da gobe mai kyau ga matasan Najeriya.
Yaushe za a yi taron matasan kasar?
Dayo Israel ya bayyana cewa za a yi taron ne a tsawon kwanaki uku, daga ranar 3 zuwa 5 ga Satumba a fadar shugaban kasa.
Shugaban matasan ya tabbatar da cewa shugaban kasa Bola Tinubu na cikin waɗanda za su yiwa matasan Najeriya bayani na musamman a yayin taron.
Wa za a gayyata taron matasan Najeriya?
Rahoton Business Day ya nuna cewa Israel ya ce taron zai hada da matasa daban daban a Najeriya ciki har da ma'ikatan gwamnati ta masu zaman kansu.
Ya kara da cewa matasan za su zanta da ministoci tare da yin bayani da ba da shawara kan harkokin ilimi, tattali, kimiyya da fasaha da sauransu.
Yan APC sun nemi taimakon Ganduje
A wani rahoton, kun ji cewa matsayin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya sa wasu yankunan kasar nan sun fara neman daukinsa.
Kungiyar kishin APC a jihar Enugu ta nemi Ganduje ya gaggauta shiga tsakani domin warware barazanar masu cin amanar jam'iyyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng