'Yan Bindiga Sun Dauki Mummunan Mataki kan Jami'in Tsaron da Suka Sace a Plateau

'Yan Bindiga Sun Dauki Mummunan Mataki kan Jami'in Tsaron da Suka Sace a Plateau

  • Ƴan bindiga sun hallaka jami'in ɗan sandan da suka yi garkuwa da shi a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Jami'an tsaron wanda aka yi garkuwa da shi an gano gawarsa ne a cikin daji a ranar Lahadi, 18 ga watan Agustan 2024
  • Rundunar ƴan sandan jihar Plateau ba ta fito ta fitar da wata sanarwa ba kan kisan da aka yiwa jami'in ɗan sandan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - 'Yan bindiga sun hallaka jami'in ɗan sandan da suka yi garkuwa da shi a jihar Plateau.

Ƴan bindigan sun sace jami'in ɗan sandan ne a wajen ƙauyen Kampani da ke gundumar Bashar a ƙaramar hukumar Wase ta jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka babban kwamandan Boko Haram, hotuna sun fito

'Yan bindiga sun hallaka dan sanda a Plateau
'Yan bindigan sun hallaka dan sandan da suka sace a Plateau Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An gano gawar ɗan sandan

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an ga gawar jami'in tsaron ne a cikin daji a ranar Lahadi, 18 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan sun sace jami'in ɗan sandan ne lokacin da yake tafiya tare da wani soja bayan sun yi musu kwanton ɓauna a kusa da ƙauyen Kampani.

Yayin da sojan ya samu ya tsira, jami'an ɗan sandan ya faɗa hannun ƴan bindigan.

Majiyoyi daga garin Wase sun tabbatar da cewa an gano gawar ɗan sandan a cikin wani daji da ke Bangalala a ranar Lahadi.

Ƴan bindiga dai na yawan kai hare-hare cikin yan kwanakin nan a ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar Wase.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Plateau, DSP Alabo Alfred, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kara karanta wannan

Kwamishinan da 'yan bindiga suka sace kan hanyar zuwa daurin aure ya kubuta

Sai dai, kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa bai samu rahoto ba kan lamarin har zuwa yanzu.

"Gaskiya ba ni da wani rahoto a kan hakan."

- DSP Alabo Alfred

Ƴan bindiga sun sace ƴan China

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu ƴan ƙasar China biyu a yankin ƙauyen Kemta da ke kan titin Onigbedu a ƙaramar hukumar Ewekoro ta jihar Ogun.

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ƙara da cewa jami'an tsaro na ƙoƙarin ceto su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng