Dakarun Sojoji Sun Hallaka Babban Kwamandan Boko Haram, Hotuna Sun Fito

Dakarun Sojoji Sun Hallaka Babban Kwamandan Boko Haram, Hotuna Sun Fito

  • Dakarun sojojin Najeriya masu yaƙi da ƴan ta'adda sun samu gagarumar nasara a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai na CJTF sun hallaka wani kwamandan Boko Haram da wasu ƴan ta'adda mutuum biyu
  • Jami'an tsaron sun kuma ƙwato makamai a hannun ƴan ta'addan bayan sun yi musayar wuta a dajin Sambisa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun samu nasarar hallaka kwamandan ƴan ta'addan Boko Haram mai suna Abu Rijab.

Dakarun sojojin sun kuma hallaka ƴan ta'addan na Boko Haram guda biyu a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Sojoji sun hallaka kwamandan Boko Haram
Sojoji sun hallaka kwamandan Boko Haram da wasu 'yan ta'adda Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Zagazola Makama wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya tabbatar da hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a jihar Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka hallaka ƴan Boko Haram

Zagazola ya ce dakarun sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai na CJTF sun kai wani samame a ranar Asabar a sansanin ƴan ta'addan da ke yankin Bula Daloje na ƙaramar hukumar Bama.

Masanin kan harkokin tsaron ya ce majiyoyin sirri sun tabbatar da cewa ƴan ta'addan sun yiwa sojojin kwanton ɓauna a kan hanyarsu ta zuwa maɓoyarsu, wanda hakan ya sanya aka yi ƙazamin musayar wuta.

Dakarun Sojojin sun yi nasarar daƙile harin, inda suka kashe ƴan ta'addan tare da tilastawa sauran tserewa.

Sai dai, ɗaya daga cikin jami’in na rundunar haɗin gwiwa ya samu raunukan harbin bindiga inda daga baya ya rasa ransa.

Sojojin sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da wayar hannu a yayin samamen.

Sojoji sun hallaka ƴan bindiga

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fayyace gaskiya kan wani sharri da aka dade ana yi masa

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadarin Daji (OPHD), sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun hallaka ƴan bindiga biyu a ci gaba da yaƙin da suke yi da miyagu masu tayar da ƙayar baya a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng