Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Jihar Zamfara

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Jihar Zamfara

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri na miyagun ƴan bindiga a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Sojojin na rundunar Operation Hadarin Daji sun yi nasarar sheƙe ƴan bindiga mutum biyu bayan sun yi musayar wuta
  • Kakakin rundunar wanda ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa an kuma ƙwato babur guda ɗaya a hannun ƴan bindigan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadarin Daji (OPHD), sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun hallaka ƴan bindiga biyu a ci gaba da yaƙin da suke yi da miyagu a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari ana tsakiyar shagalin biki, sun tafka mummunar ɓarna

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Zamfara
Sojoji sun hallaka 'yan bindiga biyu a jihar Zamfara Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Sojoji sun hallaka ƴan bindiga a Zamfara

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kakakin rundunar, Laftanar Sulaiman Omale, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 18 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin ya bayyana cewa dakarun sojojin ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar TM Opurum sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga biyu yayin musayar wuta a Kauran Namoda.

Sanarwar ta ƙara da cewa jami'an tsaron sun kai ɗauki cikin gaggawa bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ƴan bindigan a Unguwar Sarkin Musulmi cikin ƙaramar hukumar Kauran Namoda.

Omale ya ƙara da cewa bayan sojojin sun isa wurin, sun yi musayar wuta da ƴan bindigan inda suka hallaka biyu daga cikinsu yayin da sauran suka tsere.

Bayan fatattakar ƴan bindigan, sojojin sun kuma ƙwato babur guda ɗaya da suke amfani da shi.

Karanta wasu labarin kan sojoji

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan 'yan bindiga sun hallaka basarake a jihar Arewa

Ƴan ta'adda sun farmaki sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta’adda ɗauke da miyagun makamai sun kashe sojoji huɗu a ƙaramar hukumar Gudu da ke jihar Sokoto.

Ƴan ta'addan sun yi wa sojojin kwanton ɓauna ne a hanyar Kukurau zuwa Bangi yayin da suke sintiri da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Asabar, 10 ga watan Agustan 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng