Tinubu Ya Fara Daukar Matakin Tsuke Bakin Aljihun Gwamnati
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci rage yawan tawagar Najeriya da za ta halarci taron majalisar ɗinkin duniya (UNGA) da za a yi a Amurka
- Shugaba Tinubu ya umarci waɗanda ba su da abin yi a wajen taron karo na 79 da za a yi a birnin New York kada su halarta
- Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila wanda ya bayyana umarnin ya ce an ɗauki matakin ne domin tsuke aljihun bakin gwamnati
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya gargadi jami’an gwamnati da shugabannin hukumomi dangane da taron majalisar ɗinkin duniya (UNGA) karo na 79 da za a yi.
Shugaba Tinubu ya gargaɗi waɗanda ba su da wani abu da za su yi a wajen taron wanda za a yi a birnin New York na ƙasar Amurka, da kada su halarta.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana wannan umarni, a cikin wata sanarwa da shafin PBAT Media Centre ya sanya a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a wajen wani taron bita na kwana ɗaya da hukumar gudanarwar fadar shugaban ƙasa ta shiryawa shugabannin hukumomin gwamnati da ke ƙarƙashinta, ranar Asabar.
Meyasa Tinubu ya rage yawan tawagar?
Gbajabiamila ya ce matakin rage tawagar Najeriya zuwa wajen taron na UNGA a watan Satumba, na daga shirin gwamnati na tabbatar da cewa ana kashe kuɗi ta hanyar da suka dace da tsuke aljihun gwamnati.
"A lokacin zanga-zangar kwanan nan da aka yi, akwai maganganun gwamnati ta tsuke aljihun bakinta. Kowa ya zura ido ya ga Najeriya kamar yadda ta saba a baya za ta tura tawaga mafi girma zuwa UNGA."
"Bisa abin da ke faruwa a baya, mun san cewa wasu mutane suna amfani da irin waɗannan tarurrukan na ƙasa da ƙasa wajen yin harkokin gabansu."
"Na samu umarni daga shugaban ƙasa cewa a wannan karon za mu ɗauki mataki. Idan baka da wani abin yi a wajen taron UNGA, kada ka je Amurka, wannan umarni ne daga shugaban ƙasa."
- Femi Gbajabiamila
Farfesa ya caccaki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shahararren farfesan tarihi, Toyin Falola, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gaza magance manyan matsalolin da suka haddasa zanga-zangar #EndBadBadGovernance.
Farfesan ya bayyana cewa Tinubu bai yi magana kan hanyoyin magance yunwa, tsadar rayuwa da rashin tsaro waɗanda su ne suka haifar da zanga-zangar ba.
Asali: Legit.ng