An Samu Asarar Rai Bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki 'Yan Sanda a Shingen Bincike

An Samu Asarar Rai Bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki 'Yan Sanda a Shingen Bincike

  • Ƴan bindiga sun farmaki wani shingen binciken ƴan sanda a ƙaramar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra da ke yankin Kudu maso Gabas
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka jami'in ɗan sanda ɗaya bayan sun buɗe musu wuta suna tsaka da gudanar da aikinsu
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce ana ƙoƙarin cafke miyagun

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Wasu ƴan bindiga sun kai hari a shingen binciken ƴan sanda a jihar Anambra.

Ƴan bindigan sun farmaki shingen binciken ne da ke kusa da ofishin ƴan sanda na Nnobi a kan titin hanyar Nnobi/Nkpor a ƙaramar hukumar Idemili ta Kudu a jihar.

Kara karanta wannan

Yadda shugabannin 'yan bindiga ke jagorantar zaman lafiya a Zamfara

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda a Anambra
'Yan bindiga sun hallaka dan sanda a Anambra Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ce wannan harin na baya-bayan na zuwa ne ƙasa da sato uku bayan ƴan bindiga sun farmaki wani shingen binciken ƴan sanda a jihar inda suka hallaka ɗan sanda ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya da ke kusa da inda ƴan bindigan suka harin ta ce an hallaka jami'in ɗan sanda ɗaya. Majiyar ta ƙara da cewa jami'in ɗan sandan shi ne direban ɗaya daga motocin ƴan sandan.

Me ƴan sanda suka ce kan harin?

Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Anambra, SP Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

SP Ikenga Tochukwu ya bayyana cewa jami'an ƴan sandan suna tsaka da aikin ido kan ababen hawa ne lokacin da ƴan bindigan suka kai musu farmaki.

Ikenga ya kuma bayyana cewa al'amura sun daidaita a yankin yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin cafko miyagun bisa umarnin kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Nnaghe Itam.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun sace jami'in dan sanda

Ƴan bindiga sun kashe shugaban makaranta

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla fasinjoji bakwai da suka hada da shugaban makaranta da direba sun mutu a kauyen Sai da ke kan hanyar Takum zuwa Wukari a jihar Taraba.

Wasu fusatattun matasa sun kashe wasu mutum uku a garin Takum, hedikwatar karamar hukumar Takum ta jihar Taraba, sakamakon kisan matafiyan

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng