Majalisa Ta Dauki Matakin Kawo Karshen Barayin Man Fetur a Najeriya
- Shugaban kwamitin musamman na majalisar wakilai kan satar man fetur ya yi gargaɗi kan masu ƙoƙarin durƙusar da tattalin arziƙin ƙasar nan
- Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa lokacin satar man fetur ya zo ƙarshe a ƙasar nan domin ba za su bari a ci gaba ba
- Ado Doguwa ya nuna cewa duk wanda aka samu da hannu a satar ɗanyen man fetur za su fuskanci fushin hukuma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kwamitin musamman na majalisar wakilai kan satar ɗanyen man fetur ya yi gargaɗi kan ɓarayin mai a ƙasar nan.
Kwamitin ya yi gargaɗin cewa lokacin satar ɗanyen man fetur a ƙasar ya ƙare domin duk wanda aka samu da hannu a ciki zai fuskanci fushin doka.
Shugaban kwamitin Alhaji Alhassan Ado Doguwa ne ya yi wannan gargaɗin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a hukunta ɓarayin man fetur a Najeriya
Ya bayyana cewa shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya umarce su da su gano abin da ke haddasa irin ɓarnar da ake yi ɓangaren man fetur da iskar gas na ƙasar nan.
Ado Doguwa ya bayyana cewa ba za su zauna su zura ido su bari ɓarayin man fetur su ci gaba da kawo matsaloli ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba.
"Ba za mu bari gwamnatinmu ta Tinubu ta ci gaba da ciyo basussuka ba sakamakon satar da ake yi a ɓangaren man fetur da iskar gas."
"Wannan abin takaicin yana faruwa ne saboda fasa bututun mai a yankin Neja Delta, kuma ya zama dole a kawo ƙarshen hakan."
"Kwamitin ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa domin ceto gwamnatin Tinubu daga waɗannan abubuwan marasa daɗi da ake yi a yankunan da ake haƙo man fetur."
"Za mu tabbatar da cewa wannan kwamitin ya zaƙulo masu laifin tare da ƴan siyasan da ke goya musu baya."
- Alhaji Alhassan Ado Doguwa
Kuɗin da aka kashe wajen yaƙi da ɓarayin mai
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kashe sama da dala biliyan 1.5 daga shekarar 2020 zuwa yau domin kare gidajen man kasar da kuma dakile satar danyen mai.
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ne ya bayyana hakan a wajen taron jin ra’ayin jama’a na majalisar wakilai kan satar danyen mai.
Asali: Legit.ng