Yadda Shugabannin 'Yan Bindiga Ke Jagorantar Zaman Lafiya a Zamfara

Yadda Shugabannin 'Yan Bindiga Ke Jagorantar Zaman Lafiya a Zamfara

  • Zaman lafiya na ci gaba da dawowa a wasu daga cikom ƙauyukan da suka kasance a ƙarƙashin ikon ƴan bindiga a Zamfara
  • Shugabannin ƴan bindiga huɗu da suka haɗa da Ado Alero, Bello Turji, Dogo Gide da Dankarami sun yi sulhu da mutanen yankunansu
  • Sai dai, har yanzu wasu ƴan bindigan da ke a wasu yankunan jihar na ci gaba da gallazawa mutanen da ke rayuwa tare da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Sannu a hankali zaman lafiya na ci gaba dawowa a wasu ƙauyukan da ƴan bindiga ke riƙe da su a jihar Zamfara.

Hakan ya faru ne sakamakon sulhu da shugabannin ƴan bindiga suka yi da mutanen waɗannan ƙauyukan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari ana tsakiyar shagalin biki, sun tafka mummunar ɓarna

'Yan bindiga na jagorantar sulhu a Zamfara
Wasu 'yan bindiga na zaune lafiya da mutane a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An yi yarjejeniya da shugabannin ƴan bindiga

Jaridar Leadership ta rahoto cewa shugabannin ƴan bindiga huɗu da ake nema ruwa a jallo ne suka samar da yarjejeniyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin ƴan bindigan su ne Ado Alero a Zamfara ta tsakiya, Bello Turji da Dankarami waɗanda ke yankin Arewa, da Dogo Gide wanda ya ke da yammacin Zamfara

Sama da ƙauyuka 100 ne a baya suka kasance a ƙarƙashin ikon ƴan bindiga a faɗin jihar.

Kowane daga cikin shugabannin ƴan bindigan daga cikin mazaɓun sanatoci uku na jihar, waɗanda ƴan asalin wajen ne, sun mayar da kansu sarakuna inda suke kafa dokoki kan mutane yadda suke so.

Bayan sauran ƙungiyoyin ƴan bindiga 30 da ke Zamfara, shugaban ƴan bindigan huɗu su ne suke da iko a ƙauyukan da ke a mazaɓun sanatoci uku na jihar.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun sace jami'in dan sanda

An samu zaman lafiya

Mutanen da ke ƙauyukan yammacin Tsafe a ƙarƙashin Ado Alero, na yankin Dansadau a ƙaramar hukumar Maru ƙarƙashin Dogo Gide da ƙaramar hukumar Shinkafi ƙarƙashin Bello Turji, sun ce suna zaune lafiya da ƴan bindiga.

Bayan zaman lafiyan da suke yi da su, har kare su suke yi daga hare-haren wasu ƴan bindigan da ba a yankin suke ba.

Mutanen sun yi amanna cewa Allah ya amsa addu'arsu domin jihar ta samu zaman lafiya kuma manoma za su samu amfanin gona mai yawa.

Sai dai, yayin da wasu ƙauyukan ke zaune cikin kwanciyar hankali da ƴan bindigan, wasu ƙauyukan da ke a hannun ƴan bindigan da ke gaba da su Dogo Gide na shan wahala a hannun ƴan bindigan.

Matawalle ya nesanta kansa da ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle, ya ja kunnen abokan adawarsa a siyasa da su guji alaƙanta shi da lamurran Bello Turji.

Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya zargi wasu a cikin gwamnatin Zamfara da shirya labarai kan matsalar tsaron jihar tare da danganta masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng