'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ana Tsakiyar Shagalin Biki, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Ana Tsakiyar Shagalin Biki, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

  • Yan bindiga sun kai mummunan hari wurin bikin gargajiya a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta Arewa a jihar Anambra
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun jikkata sama da mutum 10, kana sun tafi da wasu mutum takwas a harin
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Anambra, SP Ikenga ya ce ba shi da masaniyar kai harin a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra - Ƴan bindiga sun tarwatsa bikin al'ada na gargajiya a ƙauyen Amakor da ke yankin Nanka a ƙaramar hukumar Orumba ta Arewa a ihar Anambra.

Shagalin bikin dai ya koma tashin hankali a lokacin da maharan suka yi awon gaba da mutum takwas bayan sun raunata akalla mutane 12.

Kara karanta wannan

Shekarau ya bayyana wani babban sirrinsa kafin ya zama gwamnan Kano

Sufetan yan sandan Najeriya, IGP Kayode.
Yan bindiga sun sace mutum 8 da suka kai Hari wurin bikin gargajiya a Anambra Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Wani mai kambun Ozo, Emmanuel Ilo, wanda ya halarci taron ya ce Allah ne ya tseratar da shi ba wayonsa, kamar yadda Vanguard ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka yi ɓarna

Ya bayyana cewa ƴan sandan da ke gadin wurin sun yi ƙoƙarin daƙile harin amma ƴan bindigar suka ci ƙarfinsu.

Emmanuel Ilo ya ce:

"A lokacin da taro ya kankama kwatsam wasu ƴan bindiga suka shigo rufe da fuskoki, sun zo wurin bisa rakiyar wasu mazauna kauyen, daga zuwa suka fara farmakar mutane.
"Ba tare da wani bayani ko tattaunawa da jagororin taron ba, maharan suka fara tarwatsa kayayyaki a wurin, sun azabtar da mutane da waɗanda suka shirya bikin, sun bugi wasu a mazaƙuta."

Ya ce maharan sun tafi da kimanin mutane takwas ciki har da shugaban kauyen Amakor, Barista Obinna Ilo, Emerie Ilo, Sam Eminike, da kuma Cif Asina Okafor.

Kara karanta wannan

Jerin muhimman abubuwa 3 da Tinubu ya ƙara masu kudi daga hawa mulki zuwa yau

Emmanuel ya ƙara da cewa wasu daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya a harin, sun gudu sun ɓuya tun lokacin har kawo yanzu.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, SP Ikenga Tochukwu, ya ce bai san da faruwar lamarin ba.

Kakakin ƴan sandan ya shawarci al'ummar kauyen da su kai rahoton duk abin da ya faru caji ofis mafi kusa.

Yan bindiga sun sace kwamishinan Anambra

A wani rahoton ƴan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan matasa na jihar Anambra, Agha MBA tare da matarsa a hanyarsu ta zuwa Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa kwamishinan ya shiga hannun masu garkuwa ne a hanyar zuwa ɗaurin auren ɗiyar Gwamna Charles Soludo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262