Dattijon Kasa Ya Fadi Yadda Tallafin Tinubu ke Jawo Karuwar Talauci

Dattijon Kasa Ya Fadi Yadda Tallafin Tinubu ke Jawo Karuwar Talauci

  • Dattijon kasa a jihar Ekiti, Aare Afe Babalola ya bankado yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke kara jefa jama'a cikin matsi
  • Dattijon, wanda shi ne ya kirkiri jami'ar Afe Babalola a Ado-Ekiti ya bayyana cewa rabon tallafin abinci da gwamnati ke yi ba ya kawo sauki
  • Cif Babalola ya yi zargin cewa rabon tallafin abinci da gwamnatin tarayya ke yi na mayar da jama'a mabarata masu jiran sai an ba su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ekiti - Dattijo a jihar Ekiti, Cif Aare Afe Babalola ya zargi gwamnatin tarayya da kin daukar matakan da za su dakile talauci da yunwa da ke addabar yan kasa.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun wargaza kotu a Kano, sun jawo asarar N1bn yayin zanga zanga

Cif Babalola ya bayyana cewa matakin rabon tallafin abinci da gwamnatin ke yi ba zai haifar da da mai ido ba, sai dai ma kara dulmiya jama'a cikin bakin talauci.

Tinubu
Dattijon kasa ya fadi dalilin karuwar talauci Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro Cif Aare Afe Babalola na cewa tallafin abincin ya mayar da jama'a mabarata, wadanda ke Allah-Allah a ba su abinda za su ci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai yunwa," Babalola ya goyi bayan zanga-zanga

Dattijo Babalola ya ce 'yan kasar nan da su ka gudanar da zanga-zanga sun san abin da su ke, domin akwai yunwa da talauci a kasa, The Guardian ta wallafa wannan

Yan kasar nan sun yi zanga-zanga ta kwanaki 10 domin adawa da manufofin Bola Tinubu da su ka kara matse tattalin arziki da jawo hauhawar farashi a jihohi.

"Masu kukan yunwa a kasar nan sun yi haka ne tsakani da Allah. Ba ma bukatar sai wani ya faɗa mana akwai yunwa a kasa."

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya jaddadawa Tinubu matsayarsa, Yakasai ya fadi matsalar Najeriya

"Mutumin da ke jin yunwa zai iya komai domin bayyana damuwarsa," cewar CIf Babalola.

Tinubu ya yadda akwai yunwa a kasa

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta amince da kukan yan kasar nan na cewa akwai yunwa, sannan an shirya daukar mataki.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ya tabbatar da cewa akwai yunwa, ya bayyana shirin gwamnati na tabbatar da wadatar abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.