Kano: Ana Raɗe Raɗin Tsige Ganduje, Hadimin Abba Ya Maka APC a Gaban Kotu
- Shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi ya maka jami'yyar APC a gaban kotu kan zargin wawushe tallafin abinci
- Kungiyar hadin kan matasan APC a bangaren Arewa ne ta fara kai karar Shehu Wada Sagagi ga hukumar EFCC kan tallafin kayan abinci
- A jiya Alhamis, 15 ga watan Agusta kotu ta fara zama domin sauraron shari'ar shugaban ma'aikatan da kungiyar jami'yyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi ga shigar da kungiyar APC kara kotu kan zargin cinye tallafin abinci.
Matasan jam'iyyar APC ne suka zargi shugaban ma'aikatan da cinye tallafin abinci da za a raba ga talakawan jihar Kano.
Legit ta gano yadda aka yi zaman kotu kan lamarin a cikin sakon da daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC da zargin wawushe tallafin abinci
Wasu matasan jam'iyyar APC sun kai shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano wajen hukumar EFCC.
Yan APC sun zargi Shehu Wada Sagagi da karkatar da abincin da gwamnatin tarayya ta turo Kano zuwa wani waje na daban.
Shehu Sagagi ya kai APC kara kotu
Shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano ya kai karar jam'iyyar APC kan cewa za su bata masa suna a kan zargin da suka masa.
A zaman kotun da ta yi a ranar Alhamis ta ba Shehu Wada Sagagi kariya daga kamun hukuma kuma ta daga shari'ar zuwa 3 ga watan Satumba.
Sagagi: 'NNPP ba ta baba-kere'
Shehu Wada Sagagi ya bayyana cewa gwamnatin NNPP tana gudanar da ayyukanta ne a bayyane ba tare da boye boye ba.
Sagagi ya kara da cewa matasan sun fito da zargin ne domin bata masa suna da jam'iyyar NNPP a jihar Kano.
An soki Abba kan batan takardun Ganduje
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na shan kakkausar suka kan sace takardun shari'ar shugaban APC, Abdullahi Ganduje.
Tsohon kwamishinan ayyukan jihar Kano, Muaz Magaji na cikin waɗanda suka yi martani mai zafi ga gwamna Abba Kabir Yusuf kan lamarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng