Gwamna Ya Tattago Aikin Titi, Ya Toshe Hanyar Shiga Sakatariyar APC Ana Shirin Taro

Gwamna Ya Tattago Aikin Titi, Ya Toshe Hanyar Shiga Sakatariyar APC Ana Shirin Taro

  • Gwamnan Benue, Hyacinth Alia ya haramtawa tsagin APC karkashin Austin Agada gudanar da taron majalisar zartarwar jam'iyyar a jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ta kaddamar da aikin gina titi a inda sakatariyar APC ta ke, wanda ya tsohe kofar shiga ciki
  • Gwamna Hyacinth Alia ya jaddada cewa babu wani taron jam'iyyar APC da zai gudana a Benue ba tare da izininsa ba kasancewarsa jagora

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Gwamnatin Benue ta tattago aikin gina titi a gaban sakatariyar APC na jihar yayin da wani tsagin jam'iyyar ke shirin gudanar da taro.

Gwamnan Benue, Hyacinth Alia ya gargadi tsagin APC karkashin Austin Agada da ya guji gudanar da wannan taron da ya shirya yi.

Kara karanta wannan

"Idan aka zabe ni": Dan takarar gwamnan APC ya fadi babban aikin da zai yi a kwana 100

Gwamna Hyacinth Alia ya yi magana kan taron wani tsagin APC a Benue
Gwamnatin Benue ta toshe kofar shiga sakatariyar APC da aikin titi ana shirin taro. Hoto: @HyacinthAlia
Asali: Facebook

Aikin titi ya toshe kofar sakatariyar APC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu gudanar da aikin titin sun tula duwatsu a gaban kofar shiga sakatariyar, wanda ya toshe hanyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, an ce tun a safiyar ranar Alhamis jami'an tsaro sun yi wa ofishin sakatariyar APC da ke titin J.S Tarka a Makurdi kawanya.

Wata majiya ta ce wasu matasa dauke da gorori ne suka yi cincirindo a kan titin inda suke karkatar da ababen hawa zuwa hanyar kasuwar titin jirgin kasa.

Gwamna ya hana taron tsagin APC

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Tersoo Kula ya fitar, Gwana Alia ya ce ba shi da masaniyar wani taron majalisar zartarwa na jam'iyyar karkashin Mista Agada.

"Don haka gwamnan ya soke wannan taro, kuma ya ce zai dauki mataki mai tsauri kan duk wani mutum ko kungiya da suka nemi tayar da zaune tsaye a jihar."

Kara karanta wannan

NEC: Ana rade radin kwace kujerar Ganduje, APC ta tsaida ranar taron da ake jira

- Tersoo Kula

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa jaddada ikonsa na zama jagoran APC a jihar Benue, inda ya ce babu wani taron jam'iyyar da zai iya gudana ba tare da amincewarsa ba.

Yan sanda sun mamaye sakatariyar APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa dakarun 'yan sanda na sashen yaki da masu tada tarzoma sun kwace iko da sakatariyar jam'iyyar APC na jihar Benue da ke Makurdi.

Ƴan sanda sun mamaye sakatariyar wadda ke ƙarƙashin jagorancin Kwamared Austin Agade yayin da tsagin jam'iyyar ke shirin rantsar da kwamitin tsare-tsaren zabe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.