Hankula Sun Tashi Bayan 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Jami'in Dan Sanda

Hankula Sun Tashi Bayan 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Jami'in Dan Sanda

  • Wasu ƴan bindiga a jihar Plateau sun yiwa jami'an tsaro kwanton ɓauna lokacin da suke cikin tafiya a kan hanyarsu ta zuwa wani ƙauye
  • Ƴan bindigan sun sace wani jami'an ɗan sanda a yayin harin inda suka tafi da shi zuwa cikin daji a yammacin ranar Laraba
  • Majiyoyi sun bayyana cewa tawagar jami'an tsaro ta bi sahun ƴan bindigan zuwa maɓoyarsu domin kuɓutar da ɗan sandan daga hannunsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani jami’in ƴan sanda a jihar Plateau.

Ƴan bindigan sun sace jami'in ɗan sandan ne a kusa da ƙauyen Kampani da ke ƙaramar hukumar Wase a jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Jami'an 'yan sanda 181 sun samu karin girma a Kano, kwamishina ya ja hankalinsu

'Yan bindiga sun sace dan sanda a Plateau
'Yan bindiga sun sace jami'in dan sanda a Plateau Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yadda ƴan bindiga suka sace ɗan sanda

Jaridar Daily Trust ta ce wata majiya ta shaida mata cewa lamarin ya auku ne da yammacin ranar Laraba, 14 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce ƴan bindiga sun sace ɗan sandan ne bayan sun yi musu kwanton ɓauna lokacin da suke tafiya tare da wani soja a kan hanyar zuwa ƙauyen Kamfani daga ƙauyen Zurak.

Majiyar ta ce yayin da aka sace ɗan sandan, sojan ya samu ya tsere.

Jami'in ɗan sandan da sojan na aiki ne tare da tawagar jami’an tsaro da ke aiki a ƙauyukan Bangalala, Kampani, da Zurak waɗanda ƴan bindiga suka addaba.

Majiyoyi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Wani shugaban matasa a yankin mai suna, Sahabi Sambo, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

"Dukkansu su biyun suna hanyar zuwa Kampani ne wajen abokan aikinsu amma sai aka kai musu hari a kan hanyarsu. Har yanzu ba mu ji komai ba dangane da inda ɗan sandan yake."

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan 'yan bindiga sun hallaka basarake a jihar Arewa

- Sahabi Sambo

Shugaban matasan ya ƙara da cewa jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji, ƴan sanda da ƴan sa-kai, sun bi sahun ƴan bindigan zuwa maɓoyarsu a ranar Alhamis domin ceto ɗan sandan.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Alabo Alfred kan lamarin.

Kakakin ƴan sandan ya ce bai samu rahoto ba kan lamarin amma zai bincika ya gani.

"Ban samu wani rahoto irin wannan ba, amma zan bincika."

- DSP Alabo Alfred

Ƴan bindiga sun hallaka basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ƴan bindiga sun kashe wani basaraken gargajiya, Onu na garin Itama da ke ƙaramar hukumar Dekina a jihar Kogi.

Miyagun ƴan bindigan wadanda ke ɗauke da makamai sun hallaka mai martaba, Shagari Ebije’ego Job, bayan sun farmasa har cikin gidansa da ke garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng