Sace Takardun Shari'a: Ganduje Ya Yi wa Gwamna Abba Martani Mai Zafi

Sace Takardun Shari'a: Ganduje Ya Yi wa Gwamna Abba Martani Mai Zafi

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, ya fito ya yi martani ga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan zargin sace takardun shari'ar da ake yi masa
  • Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana zargin a atsayin mara tushe ballantana makama wanda babu wani mai hankali da zai yarda da shi
  • Shugaban na APC ya ce ruwa ne ya ƙarewa ɗan kada, shiyasa gwamnan yake ta ƙoƙarin jifarsa da zarge-zargen cin hanci da rashawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da mayar da mulki wani babban abin dariya.

Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan iƙirarin gwamnan na cewa an sace takardun kotu na shari'ar da ake yi masa kan zargin cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Ana zargin batar takardun shari'a, Ganduje ya fadi wanda ya dauki nauyin zanga zanga

Ganduje ya caccaki Gwamna Abba
Ganduje ya yi martani kan zargin sace takardun shari'arsa Hoto: Abdullahi Umar Ganduje, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Sai dai da yake mayar da martani kan kalaman na Gwamna Abba, Ganduje ya ce zargin da gwamnan ya yi ba ya da tushe ballantana makama, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani Ganduje ya yi wa Abba?

Martanin na Ganduje na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Edwin Olofu, ya fitar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Akwai ban dariya yadda aka mayar da mulki a Kano wani abin wasa inda gwamnatin jiha za ta ɓata ƙimarta ta hanyar zargin cewa masu zanga-zanga sun shiga kotu sannan sun sace takardun shari'ar shugaban APC a wannan zamanin na fasaha da muke ciki."
"Babu wani mai hankali da zai yarda da wannan farfagandar. Me ya samu takardun da ke hannun lauyoyin gwamnati?"
"A bayyane yake gwamnatin ba ta san yadda za ta gudanar da mulkin jihar ba, wanda hakan ya sanya a koda yaushe take ƙirƙiro zarge-zargen cin hanci kan Ganduje da iyalansa waɗanda suka yi wa jihar hidima."

Kara karanta wannan

Gwamna ya jingine Atiku, ya faɗi mutum 1 da ya kamata ya karɓi mulkin Najeriya a 2027

"Wannan iƙirarin ba komai ba ne face ƙoƙarin Gwamna Abba na son kawar da hankalin mutane daga hannun da yake da shi a rikicin da ya auku a jihar."

-Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje na iya rasa muƙaminsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa an fara hasashen Shugaba Bola Tinubu zai iya sauyawa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje mukami.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ƙasan zai iya mayar da tsohon gwamnma na Kano a matsayin jakada a kowace ƙasa da ke Nahiyar Afirka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng