Arangama Tsakanin Manoma da Makiyaya Ta Jawo Asarar Rayuka a Adamawa

Arangama Tsakanin Manoma da Makiyaya Ta Jawo Asarar Rayuka a Adamawa

  • An kara samun sabani tsakanin manoma da makiyaya a Arewacin kasar nan, wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi
  • Wannan karon, sabanin ya afku ne a jihar Adamawa, inda rikicin da ya faro kamar wasa ya fantsama zuwa wasu kauyuka
  • Rikicin ya faru a karamar hukumar Demsa inda aka kashe mutane 3, tare da jikkata wasu, amma jagorori sun shiga batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa - An samu rikici tsakanin makiyaya da.manoma a jihar Adamawa da ke Arewacin Najeriya.

Barakar ta afku a karamar hukumar Demsa, kuma ta lakume rayukan mutane uku, wasu mutum takwas sun jikkata yayin da aka shiga zullumi.

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya jaddadawa Tinubu matsayarsa, Yakasai ya fadi matsalar Najeriya

Manoma
Rikicin manoma da makiyaya ya kashe mutane 3 a Adamawa Hoto: David Silbeberg
Asali: Getty Images

Jaridar The Nation ta tattaro cewa rikicin ya faro daga kauyen Kodomun, sannan ya fallatsa zuwa Kudiri, Sabonlayi, Kwayine, da Gorogbakai a karamar hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano dalilin rikicin manoma da makiyayan

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa fadan tsakanin manoma da makiyayan ya samo asali ne daga rade-radin wasu makiyaya sun kashe matashi a Kodomun.

Labarin kisan ya tayar da hankula, wanda ba a tsaye llata lokaci ba mummunan neman fansa ya kutsa wasu kauyuka a Demsa.

'Yan sanda sun magantu kan rikicin

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da afkuwar tashin hankali a karamar hukumar Demsa tsakanin makwabtan juna - manoma da makiyaya

Kakakin rundunar, Suleiman Nguroje ya shaidawa manema labarai cewa tuni aka aika jami'an tsaro, kuma sun kwantar da tarzomar.

Haka kuma manyan garin sun tsoma bakin a cikin lamarin domin ayi sulhu tsakanin masu rikicin da dakatar da zubar da jini.

Kara karanta wannan

Jigawa: Wasu matasa 2 sun mutu a yanayi mai ban tausayi a hanyar zuwa Kasuwa

Rikicin manoma da makiyaya ya jawo asara

A wani labarin kun ji cewa rikici ya kacame tsakanin manoma da.makiyaya a jihar Jigawa,wanda ya jawo asarar rayukan mutane uku da jikkata wasu da dama.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, DSP Lawan Shiisu Adam da ya tabbatar da rikicin ya ce an samu sabani ne a kan gandun dajin Baranda a karamar hukumar Kiyawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.