Karon Farko a Watanni 19: Farashin Kayan Abinci Ya Sauko, NBS Ta Yi karin Bayani

Karon Farko a Watanni 19: Farashin Kayan Abinci Ya Sauko, NBS Ta Yi karin Bayani

  • Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce hauhawar farashin kayayyaki musamman na abinci ya ragu zuwa kashi 33.40% a Yuli
  • Wannan sabon rahoton na hukumar NBS na nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta ragu sosai a karon farko cikin watanni 19
  • Farashin kifi, dodon kodi, dabino, kankana, garri, littattafai, nama da dai sauran wasu kayayyakin abinci ya sauka, inji rahoton

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu zuwa kashi 33.40 a watan Yuli, kasa da kashi 34.19 da aka ruwaito a watan Yuni.

Wannan ci gaban shi ne na farko da aka samu tun daga Disamba, 2022, lokacin da mizanin hauhawar farashin ya ragu zuwa kashi 21.34.

Kara karanta wannan

Arangama tsakanin manoma da makiyaya ta jawo asarar rayuka a Adamawa

NBS ta fitar da rahoton hauhawar farashin kayayyaki na watan Yulin 2024
Rahoton NBS ya nuna faduwar hauhawar farashin kayan abinci a watan Yuli. Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Rahoton hauhawar farashin kayayyakin CPI

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa a ma'aunin CPI (wanda ke auna yawan sauyin farashin kayayyaki da ayyuka), NBS ta ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu da kashi 0.8 cikin dari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta ce mizanin hauhawar farashin kayayyaki na cikin tattalin arziki a watan Yuli ya nuna raguwar kashi 0.3 idan aka kwatanta da farashin a watan Yunin 2024.

"Mizanin hauhawar farashin kayayyaki na shekara ya karu da kashi 9.32 idan aka kwatanta da farashin da aka samu a watan Yulin 2023, wanda ya kasance kashi 24.08."

- A cewar rahoton NBS.

Farashin kayan abinci ya fadi

Hukumar NBS ta kuma ce hauhawar farashin kayan abinci a watan Yuli ya ragu zuwa kashi 39.53, idan aka kwatanta da kashi 40.87 a watan Yuni, in ji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Ya haura miliyan 20: Sanata Kawu Sumaila ya fadi albashin da ya ke karba duk wata

A ma'aunin wata wata, hauhawar farashin abinci a watan Yulin 2024 ya kai 2.47 wanda ke nuna raguwar kashi 0.08 idan aka kwatanta da farashin da aka samu a watan Yunin 2024 (kashi 2.55).

Ana iya danganta faɗuwar farashin kayan abinci da yadda karin kudin wasu kayayyaki ya gaza samun karbuwa, kamar su madarar gwangwani, madarar jarirai, da dai sauransu.

Farashin kifi, dodon kodi, dabino, kankana, garri, littattafai, nama da dai sauran wasu kayayyakin abinci ya sauka da kashi 39,53 a watan Yuli.

NBS: An samu karin hauhawar farashi

A wani labarin na daban, hukumar NBS ta ce farashin kayayyaki a Najeriya ya yi tashin gwauron zabi inda ya kai kashi 34.19 a watan Yunin 2024, daga kashi 33.95% a watan Mayu.

Kamar yadda hukumar ta ce, hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 40.87% a watan Yuni yayin da farashin kayan abinci da kayan sha suka cigaba da tashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.