Hajjin 2024: Hukumar EFCC Ta Tsare Shugaban NAHCON, Ta Kwato Makudan Kudi
- Hukumar yaƙi da cin hanci da yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta tsare shugaban NAHCON da sakatarenta
- EFCC ta tsare mutanen ne kan zargin karkatar da tallafin N90bn da gwamnatin tarayya ta ba da domin aikin Hajjin 2024
- A binciken da hukumar ta fara kan jami'an na NAHCON, ta ƙwato SR314,098 waɗanda suka kusa N131m a kuɗin Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta tsare shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON), Jalal Arabi da sakataren hukumar Abdullahi Kontagora.
Hukumar EFCC ta tsare su ne bisa zargin karkatar da tallafin N90bn da gwamnatin tarayya ta bayar domin Hajjin bana na shekarar 2024.
Nawa EFCC ta ƙwato daga jami'an NAHCON?
Jaridar The Punch ta ce a cikin wata takarda da wakilinta ya gani a ranar Laraba, hukumar EFCC ta ce ta ƙwato jimillar SR314,098 (kusan N131m).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An karbo wadannan kudi ne daga hannun shugaban NAHCON da sauran manyan jami’ai.
Zargin da ake yi wa shugabannin NAHCON
Hukumar EFCC ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa daga cikin N90bn na tallafin, Jalal Arabi, ya biya kansa da sauran jami'an kuɗin da suka wuce ƙa'ida.
Shugaban ya kamata ya samu SR15,929 amma ya samu SR50,000, kwamishinoni uku da ya kamata su samu SR 15,929 kowannensu ya samu SR 40,000.
Sakataren ya samu SR 30,000 maimakon SR14,336, daraktoci/shugaban ma'aikata sun karɓi SR 30,000 maimakon SR2,550 da ya kamata su samu.
Daga ƙarshe hukumar EFCC ta ƙwato jimillar SR314,098 daga hannunsu.
EFCC na bincike kan tallafin N90bn
A ranar Laraba, wata majiya a hukumar ta EFCC ta bayyana cewa an sake gayyatar shugaban NAHCON a ranar Laraba domin amsa tambayoyi kuma an tsare shi.
"Sakataren da shugaban hukumar suna hannunmu kuma suna fuskantar tambayoyi kan tallafin N90bn, da sauran zarge-zarge."
- Wata majiya
Wata takarda ta nuna cewa har yanzu tsabar kuɗin SR 8,614,175.27 da aka cire daga cikin tallafin N90bn da gwamnatin tarayya ta ba hukumar NAHCON, ba a san inda suka yi ba.
ICPC ta kai samame hedkwatar NAHCON
A wani labarin kuma, kun ji hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC ta kai samame hedikwatar hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) a birnin tarayya Abuja.
Hukumar ICPC ta kai samame hedikwatar NAHCON domin zargin karkatar da kudin tallafin aikin Hajji na N90bn da gwamnatin tarayya ta ba da.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng