Babu Haraji: Bayani Dalla Dalla Kan Sharuddan Shigo da Abinci Najeriya Kyauta

Babu Haraji: Bayani Dalla Dalla Kan Sharuddan Shigo da Abinci Najeriya Kyauta

  • Gwamnatin Najeriya ta yi sanarwar dauke harajin shigo da wasu nau'ukan abinci daga ƙasashen waje ba tare da biyan haraji ba
  • Hukumar kwastam ta lissafa sharuddan da yan kasuwa masu shigo da abinci daga ƙetare za su cika kafin samun cin gajiyar shirin
  • A wannan rahoton, Legit tattaro muku jerin sharuddan da gwamnatin tarayya ta gindaya da nau'ukan abincin da za a rika shigowa da su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa kan sharuddan shigo da abinci ta iyakokin Najeriya ba tare da biyan haraji ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka dokar ne domin saukaka farashin kayan abinci a Najeriya saboda saukakawa talakawa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta jero sharudan shigo da abinci daga waje ba tare da biyan haraji ba

Kayan abinci
Gwamnati ta fadi sharuddan shigo da abinci daga waje kyauta. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

A wannan rahoton mun tattaro muku muhimman bayanai kan yadda za a iya shigo da abinci kyauta daga ƙasashen ketare kamar yadda hukumar kwastam ta wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharuddan shigo da abinci Najeriya

  1. Za a shigo da abinci Najeriya ba tare da biyan haraji ba ne daga ranar 15 ga watan Yuli zuwa 31 da watan Disambar 2024.
  2. Dole kamfanin da zai shigo da kayan abinci ya kasance yana gudanar da kasuwanci a tarayyar Najeriya.
  3. Haka zalika dole kamfanin ya kasace yana aiki a Najeriya na akalla tsawon shekaru biyar da suka gabata.
  4. Bayan haka, yana daga cikin sharudda samun damar ya kasance kamfanin yana biyan haraji na shekarun da suka wuce.
  5. Abincin da za a shigo da su kyauta sun hada da shinkafa, gero, dawa, masara, alkama, da kuma wake.
  6. Kamfanin da zai shigo da shinkafa da gero dole ya kasance yana da wani kamfani da yake aikin samar da shinkafa ton 100 a kowace rana na tsawon shekaru huɗu da suke gabata.
  7. Kamfanin da zai shigo da wake, masara da alkama dole ya kasance yana da kasar noma a Najeriya tare da kamfanin sarrafa abinci.
  8. Duk kamfanin da bai cika sharuddan ba to dole zai biya haraji yayin shigo da abinci Najeriya daga kasar waje.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnati ta tona shirin dan kasar waje na kawo cikas ga mulkin Tinubu

Kwastam ta kama masu safarar mai

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da jama'a a kasar nan ke kukan rashin fetur da tsadarsa, an gano wasu masu kokarin safarar man zuwa Kamaru.

Hukumar kwastam shiyyar Adamawa/Taraba ce ta damke ganguna da jarkoki makare da fetur din a iyakar kasar nan ana shirin fita da su waje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng