Watanni 2 da Ƙara Aure a Shekara 90, Attajirin Ɗan Kasuwa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Watanni 2 da Ƙara Aure a Shekara 90, Attajirin Ɗan Kasuwa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Watanni biyu bayan ya ƙara aure, wani fitaccen attajiri a kasar Australia Richard Lugner ya riga mu gidan gaskiya
  • Rahotanni sun bayyana cewa Lugner ya mutu yana da shekaru 91 a duniya bayan ya sha fama da rashin lafiya
  • Attajirin ɗan kasuwar ya yi ƙaurin suna wajen biyan mashahuran mutane kamar irinsu Kim Kardashian da Pamela Anderson daloli don su kasance da shi a taruka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rahotanni daga ƙasar Australia sun nuna cewa fitaccen attajiri kuma biliyoniya, Richard Lugner ya mutu yana da shekaru 91 a duniya.

A cewar wasu rahotanni ranar Laraba, 14 ga watan Agusta, 2024, Lugner ya mutu ne watanni ƙalilan bayan ya angonce da mata ta shida, ƴar shekara 41 Simone Reiländer.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Simone da angonta Lugner.
Attajirin ƙasar Australia, Richard Lugner ya kwanta dama Hoto: APC Picture Desk
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Independent ta kawo a rahotonta, attajirin ɗan kasuwar ya cika ne a gidansa da ke Vienna ranar Litinin da ta shige, 12 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shahararren ɗan kasuwar dai ya riga mu gidan gaskiya ne bayan fama da rashin lafiya, kamar yadda jaridar Punch ta kawo.

Taƙaitaccen bayani game da Lugner

Lugner, ya yi shura saboda salon rayuwar sa na sharholiya, yawan aure da kuma soyayya da manyan fitattun jaruman ƴan mata na ajin farko.

Wanda ake yi wa lakabi da “Mr. Concrete,” Lugner ya kasance sananne a salon rayuwarsa kuma galibi ana ganinsa yana biki tare da manyan mutane kuma abokai.

An tattaro cewa hamshakin attajirin ya biya kudi masu nauyi ga taurari kamar Kim Kardashian, Geri Halliwell, da Paris Hilton don raka shi zuwa wasan Opera.

Amaryar Lugner ta yi jimami

Kara karanta wannan

Gwamnan ya bi hanyar lalama, ya roƙi matasa su rungumi zaman lafiya a Arewa

Amaryar marigayin kuma matarsa ta shida, Simone ta yi jimamin rasuwar angonta wanda akalla ya girme ta da shekaru kusan 50.

Ta kuma bayyana shi a matsayin "cikar burin rayuwarta," tare da wallafa wani hoton fentin marigayin.

Aduke Gold: Mawakiyar addini ta mutu

A wani rahoton kuma kun ji cewa matashiyar mawakiyar yabo na addinin Kirista a Najeriya, Aduke Ajayi ta yi bankwana da duniya a ranar Litinin da ta shige.

Marigayiyar da aka fi sani da Aduke Gold ta yi shura a fagen wakokin yabo inda al'ummar Kiristoci suka kadu da wannan rashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262