Ana Tsaka da Maganar Dan Bello, Gwamnonin Arewa Sun Saka Labule

Ana Tsaka da Maganar Dan Bello, Gwamnonin Arewa Sun Saka Labule

  • Gwamnonin Arewa sun yi zaman farko bayan zanga zanga domin neman mafita kan matsalolin da suka addabi yankinsu
  • Shugaban gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya jagoranci zaman a birnin tarayya Abuja a yammacin Laraba
  • Hakan na zuwa bayan yawaita kira da aka yi kan muhimmacin zama domin neman mafita ga matsalolin yankin Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnonin Arewa sun fara zama domin ƙoƙarin samar da mafita kan damuwowin yankinsu.

An ruwaito cewa gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya jagoranci zaman a Abuja.

gwamnonin arewa
Gwamnonin Arewa sun fara zama kan matsalolinsu. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da aka yi kan taron ne a cikin wani sako da daraktan yada labaran gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamnati ta tona shirin dan kasar waje na kawo cikas ga mulkin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiran da aka yi ga manyan Arewa

Tun bayan kammala zanga zangar tsadar rayuwa Sanata Muhammad Sani Musa ya kira ga shugabannin Arewa kan hadin kai.

Sanatan ya bukaci manyan Arewa da su hada kai wajen shawo kan matsalolin yankinsu da suka bayyana ƙarara a lokacin zanga zanga.

Gwamnonin Arewa sun fara zama

Gwamnonin Arewa sun fara zama a yau domin samo mafita kan damuwowin da suka addabi mutanensu.

Gwamnonin sun saka labule ne domin tattaunawa kan samar da zaman lafiya, hadin kai da kuma kawo cigaba.

Jerin Gwamnonin da suka halarci zaman

An ruwaito cewa gwamnonin jihohin Borno, Filato Kaduna, Borno da mataimakin gwamnan Katsina sun halarci zaman.

Sai kuma gwamnan Gombe wanda shi ne shugaban gwamnonin Arewa kuma shi ya jagoranci wannan taro da aka shirya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi abin da Tinubu ya tattauna da Buhari, shugabanni a taron magabata

Manyan Arewa sun gargadi Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa dattawan Arewa sun tura sakon gargadi ga shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan canza tsarin mulkin Najeriya da aka nemi ya yi.

Alhaji Tanko Yakasai da Farfesa Auwalu Yadudu sun bukaci shugaba Bola Tinubu ya yi taka-tsan-tsan kan maganar canza tsarin mulkin.

Hakan na zuwa ne bayan kungiyar masu kishin kasa sun bukaci shugaban kasar ya canza tsarin mulkin a ziyarar da suka kai masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng