Gwamnan PDP Ya Kare Matakinsa na Sukar Tinubu, Ya Yi Jawabi Mai Kyau

Gwamnan PDP Ya Kare Matakinsa na Sukar Tinubu, Ya Yi Jawabi Mai Kyau

  • Gwamnan jihar Bauchi ya fito ya bayyana dalilinsa na sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan halin da ake ciki a ƙasa
  • Bala Abdulkadir Mohammed ya ce ya fito ya yi kalamansa ne da zuciya daya domin tunatar da gwamnati kan nauyinta
  • Sai dai, Gwamna ya nuna kuskure ne ɗora alhakin halin da ake ciki kan gwamnatin tarayya kaɗai, kowa yana da laifi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ya fito ya kare matakin da ya ɗauka kan sukar da ya yiwa shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Gwamna Bala ya bayyana cewa sukar da ya yi wa shugaban ƙasan mai ma'ana ce kuma ya yi ta ne da zuciya ɗaya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi hanyar da za a iya raba Tinubu da mulkin Najeriya

Gwamna Bala ya caccaki Tinubu
Gwamna Bala ya yi karin haske kan sukar da ya yiwa Tinubu Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne a Bauchi ranar Laraba kafin fara taron majalisar zartaswa ta jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bala ya kawo dalilin sukar Tinubu

Gwamna Bala ya ce bai kamata a yi wa kalamansa mummunar fahimta ba, inda ya ce ya yi su ne domin farkar da gwamnatin tarayya ta rage halin ƙuncin ƴan Najeriya suke ciki.

"Na yi magana mai inganci a matsayina na ɗan adawa wanda ke da kyakkyawan nufi ga shugaban ƙasa, gwamnati da al’ummar Najeriya."
"Ban yi hakan ba domin in haifar da ɓacin rai ko kuma cin mutuncin wani ba."
"Ya kamata mu saurari koke-kokensu kan rashin shugabanci na gari da inda muka kasa share musu hawaye.
"Babu wanda ya damu, babu wanda zai saurare ka idan ka fara ƙoƙarin ɗora alhakin gazawarka kan shugabannin da suka gabace ka."

Kara karanta wannan

Gwamnan ya bi hanyar lalama, ya roƙi matasa su rungumi zaman lafiya a Arewa

- Bala Abdulkadir Mohammed

Gwamna Bala ya kuma bayyana cewa kuskure ne a ɗora alhakin halin da ake ciki kan gwamnatin tarayya, domin su ma jihohi suna da na su laifin.

Gwamna Bala ya miƙa buƙata gaban majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya miƙa sabuwar buƙata a gaban majalisar dokokin jihar.

Gwamna Bala ya aika da buƙatar tabbatar da mutane uku a matsayin kwamishinoni a gwamnatinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng