'Yan Daba Sun Wargaza Kotu a Kano, Sun Jawo Asarar N1bn Yayin Zanga Zanga

'Yan Daba Sun Wargaza Kotu a Kano, Sun Jawo Asarar N1bn Yayin Zanga Zanga

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana irin asarar da ake zargi yan daba sun yi a ma'aikatar shari'ar jihar a lokacin zanga zanga
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar gani da ido ma'aikatar shari'ar Kano domin ganewa idonsa muguwar barnar da aka yi
  • Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Haruna Isah Dederi na cikin manyan jami'an gwamnati da suka raka gwamnan zuwa ma'aikatar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano ya kai ziyara ma'aikatar shari'a bayan kammala zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana irin barnar da aka aikata a ma'aikatar shari'a da ta jawo asarar dukiya mai dimbin yawa.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun sace takardun shari’ar Ganduje a kotu lokacin zanga zanga a Kano

Abba Kabir
An lalata dukiya a kotun Kano yayin zanga zanga. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya wallafa jawabin gwamnan a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An lalata kayan N1bn a kotun Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa yan daba da suka kai hari babbar kotun jihar Kano sun lalata dukiya da ta kai Naira biliyan 1.

Rahotanni sun nuna cewa an yi kone kone da fashe fashe da suka hada da motoci a kotun a lokacin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Abba Kabir Yusuf ya ce an fasa har ofishin babba alkalin jihar Kano inda aka sace takardu masu muhimmanci da ake shari'a da su.

Daba: Abba ya shawarci matasan Kano

Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga matasan Kano kan kaucewa rudin yan siyasa masu amfani da su wajen ayyukan barna a jihar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Abba ya ziyarci wurin da aka lalata, ya daukarwa Kanawa alkawari

Gwamnan ya ce ya kamata matasa su mayar da hankali wajen koyon sana'o'i domin dogaro da kansu da gina gobe mai kyau.

A karshe gwamnan ya mika godiya ga daukacin al'ummar jihar Kano bisa hadin kai da suke ba gwamnatinsa a ko da yaushe.

An sace takardun shari'ar Ganduje

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta yi bayani kan yadda yan daba suka sace takardun da ake shari'ar Abdullahi Ganduje.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar gani da ido ma'ikatar shari'ar jihar Kano bayan kammala zanga zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng