Akwai Matsala: Farashin Litar Man Fetur Ya Yi Tashin Gwauron Zabi a Kano
- Farashin da ake siyan kowace litar man fetur a mafi yawan gidajen man da ke Kano ya yi tashin gwauron zabi
- A yanzu litar ta koma ana siyar da ita kan farashin N950 zuwa N980 yayin da gidajen mai da yawa suka rufe
- Bincike ya nuna wasu daga cikin gidajen man na siyar da shi a farashin da bai kai haka ba amma ba a cika samu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gidajen siyar da man fetur a jihar Kano sun ƙara kuɗin da ake siyar da litar man fetur.
Farashin man fetur ɗin yanzu a kasuwa ya yi tashin gwauron zabi inda ya koma tsakanin N900 zuwa N950 kan kowace lita.
Farashin litar man fetur ya ƙaru a Kano
Binciken da Legit Hausa ta yi ya nuna cewa bayan wannan ƙarin da aka samu, masu kekunan adaidaita sahu a cikin birnin na Kano sun yi ƙarin kuɗi da kusan kaso 100%.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne ƴan kwanaki bayan kammala zanga-zangar #EndBadGovernanceInNigeria# a faɗin ƙasar nan.
Galibin gidajen man da ke cikin birnin Kano sun kasance a rufe yayin da wasu tsirarun da ke siyar da man suka kasance cike da layi.
Gidajen mai sun ƙara kuɗin fetur
Ibrahim Zulkiful ya shaidawa Legit Hausa cewa gidajen man da ke aiki sun ƙara farashin daga N780 zuwa N850 kafin zanga-zanga, inda ya koma N900 zuwa N950 kan kowace lita.
"Eh man fetur ya koma N950 ko yau ma da safe a haka na sha. Gidajen man fetur da dama a kulle suke. Waɗanda suka buɗe kuma akwai layi sosai."
"Wasu gidajen man irin su Aliko da AA Rano suna siyarwa kan N720 zuwa N730 amma ba a cika samu ba."
- Ibrahim Zulkiful
Lokacin fara fitar da man fetur na Dangote
A wani labarin kuma, kun ji matatar man Dangote ta ce za ta fara samar da man fetur a cikin watan Agusta domin shiga cikin kasuwanni.
Matatar ta musanta cewa za ta ƙara ɗage fara fitar da man fetur ɗin, inda ta ba da tabbacin cewa shirin fara fitar da shi zuwa kasuwa na nan kamar yadda aka tsara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng