Jigawa: Wasu Matasa 2 Sun Mutu a Yanayi Mai Ban Tausayi a Hanyar Zuwa Kasuwa

Jigawa: Wasu Matasa 2 Sun Mutu a Yanayi Mai Ban Tausayi a Hanyar Zuwa Kasuwa

  • Wasu matasa biyu sun nutse a kududdufin bayan gari a kauyen Waza da ke ƙaramar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa
  • Hukumar tsaro NSCDC ta bayyana cewa duk da kokarin kai su asibiti da aka yi, likitoci sun tabbatar da cewa duka sun rasu
  • Rahotanni sun nuna cewa matasan sun fito ne da nufin zuwa kasuwa kamar yadda suka saba amma ajali ya riske su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Wani ibtila'i da ya zo da ƙarar kwana ya yi sanadin mutuwar wasu matasa biyu a kauyen Waza da ke karamar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa.

Matasan biyu da aka bayyana sunansu da, Abubakar Ja’a, dan shekara 20, da Abubakar Abdullahi, mai shekaru 25, sun nutse ne a cikin wani kududdufi ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ana tsadar rayuwa, an kama dattijo mai shekaru 62 yana haɗa kuɗin 'bogi'

Taswirar Jigawa.
Jigawa: Mutum biyu sun mutu a wani ɗan ƙaramin tafki a Birnin Kudu Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kamar yadda Channels tv ta tattaro, matasan sun fito ne da nufin zuwa wurin sana'arsu kamar yadda suka saba yau da kullum lokacin da ibtila'in ya rutsa da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce sun nutse ne a wani ɗan ƙaramin kududdufin bayan gari wanda bai wuce nisan kilomita ɗaya ba daga cikin kauyen Waza a jihar Jigawa.

Bayan faruwar lamarin ne mutanen kauyen Tella suka sanar da dakarun hukumar tsaron fararen hula (NSCDC) domin su kai ɗaukin gaggawa.

NSCDC ta yi koƙarin ceto matasan

CSC Muhammad Garba, shugaban hukumar NSCDC reshen karamar hukumar Birnin Kudu ya tabbatar da faruwar lamarin.

"Mun samu kiran waya da misalin karfe 11:30 na safe kuma nan take muka tura jami’an kai agaji zuwa wurin.
"Abin takaicin duk da kokarin da muka yi da kuma taimakon al’umma, mun samu nasarar ciro gawarwakin ne bayan kimanin mintuna 48 ana lalube a ruwa.

Kara karanta wannan

An shiga jimami a Arewacin Najeriya, mata da miji da 'ya'yansu 5 sun mutu bayan cin rogo

Ya ce duk da an yi hanzarin kai su asibiti mafi kusa a kauyen amma daga zuwa aka tabbatar da rai ya yi halinsa, duka matasan sun rasu.

Yadda matasan suka nutse a Jigawa

Wani bincike da aka gudanar a kan lamarin ya nuna cewa tafkin ya cika maƙil wanda ya yi sanadin nutsewar mutanen biyu, Daily Trust ta rahoto.

An kuma gano cewa Abubakar Abdullahi Damina ya yi yunkurin kubutar da abokinsa Abubakar Ja’a daga nutsewa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar su duka biyun.

Jigawa ta janye dokar hana fita

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi, ta cire dokar hana fita da ta sanya a ƙananan hukumomi takwas na jihar

Dokar hana fitan da aka sanya sakamakon rikicin da aka samu a lokacin zanga-zangar nuna adawa da halin ƙunci, yanzu an cire ta gaba ɗaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262