Ana Fama da Rikicin Kano, Gwamnati Za Ta Gurfanar da Wani Sarki a Gaban Kotu
- Sarkin Obafemi a karamar hukumar Obafemi-Owode a Ogun, Taofeek Kayode Owolabi ya shiga matsala kan rigimar fili
- Majalisar dokokin jihar Ogun ta ta umarci kwamishinan shari'a ya gaggauta gurfanar da basaraken a gaban ƙuliya
- Hakan ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin shari'a da ƙorafe-ƙorafen jama'a na majalisar a zaman ranar Talata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun - Majalisar dokokin jihar Ogun ta yanke shawarar gurfanar da Olu na Obafemi da ke ƙaramar hukumar Obafemi-Owode, Oba Taofeek Owolabi.
Majalisar ta amince da shawarin gurfanar da sarkin ne bisa zarginsa da hannu dumu-dumu a badaƙalar ƙwacen filaye a yankin masarautarsa.
Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, majalisar ta ce wannan matakin ya yi daidai da tanadin dokar yaƙi da ƙwacen filaye ta jihar Ogun 2016.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta umarci a gurfanar da Sarki
Yan majalisar sun kuma umurci Antoni-Janar kuma kwamishinan shari’a, Oluwasina Ogungbade (SAN), da ya gaggauta gurfanar da Oba Owolabi a gaban kotu.
Haka kuma sun umurci ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu da majalisar sarakunan jihar Ogun da su gaggauta dakatar da sarkin.
Ƴan majalisar sun nemi a dakatar da basaraken ne bisa zargin yunƙurin tayar da zaune tsaye ta hanyar rigimar fili a kauyen Agboro-Olatunde da jiha baki ɗaya.
Meyasa majalisa ta ɗauki mataki?
Majalisar dokokin ta ɗauki wannan matakin ne bayan kwamishinan shari'a da ƙorafe-ƙorafen jama'a ya gabatar da rahoton bincike kan ƙorafin kungiyar bunƙasa Agboro-Olatunde.
A rahoton This Day, wani saeshn rahoton kwamitin ya ce:
"Rigima ta shiga tsakanin mazauna kauyen Agboro-Olatunde da Oba Taofeek Kayode Owolabi (Sarkin Obafemi) kan wani fili da ke ƙaramar hukumar Obafemi Owode."
"Basaraken ba shi da wata takardar mallakar filin kuma abin da ya aikata ya saɓawa dokar hana kwacen filaye ta 2016."
Gwamna Ododo ya rabawa alkalai motoci
Ku na da labarin Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi, a ranar Talata, ya miƙawa alkalai karin motoci 11 da ya sayo masu domin sauƙaƙa aikinsu.
Gwamnan ya damƙawa babban alkalin jihar, Josiah Mejabi sababbin motocin a wani biki da aka shirya a filin Muhammad Buhari Square da ke Lokoja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng