Ana Tsadar Rayuwa, An Kama Dattijo Mai Shekaru 62 Yana Haɗa Kuɗin 'Bogi'
- Rundunar yan sanda a jihar Bauchi sun samu nasarar cafke wani dattijo mai shekaru 62 da ake zargi da hada kuɗin ganye
- Rahotanni sun nuna cewa an kama mutumin ne yayin da ya shiga garin Bauchi bayan ya fito daga jihar Filato a cikin motar haya
- Rundunar yan sanda ta dauki matakin magana da babban bankin Najeriya CBN domin gano sahihancin kudin da mutumin ya haɗa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta kama wani dattijo da ake zargi da hada jabun kuɗi.
Kakakin yan sanda na jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya bayyana matakin da suka dauka domin gano sahihancin kudin.
Legit ta tatttaro yadda aka kama mutumin ne a cikin wani sako da rundunar yan sanda ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dattijo ya haɗa kudin ganye a Bauchi
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa wani dattijo ya shiga motar haya daga jihar Filato zuwa Bauchi kuma ya haɗa kudin ganye a yayin da suke tafiya.
Shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa mutumin ya yi amfani da takardu ne yayin haɗa jabun kudin a cikin motar hayar.
Bauchi: Yadda aka kama mai hada kudi
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa wani mutum ne a cikin motar ya fallasa dattijon a lokacin da suka sauka a garin Bauchi.
Rahoto ya nuna cewa suna isowa garin Bauchi daga Filato sai wani a cikin motar ya nemi yan sanda fada musu abin da mutumin ya yi.
Yan sanda za su tuntubi CBN
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa a halin yanzu za ta tuntubi babban bankin Najeriya domin gano sahihancin kudin da ake zargi mutumin ya haɗa.
An zargi mutumin mai suna Tahir Ahmed da hada kudi yan Naira dubu dubu ne yayin da suke tafiya a cikin motar haya.
An kama mata da miji kan jabun kudi
A wani rahoton, kun ji cewa jami'an 'yan sanda sun kama wasu ma'aurata, Olamilekan da Oluwayemisi Oludare kan zargin raba jabun kudi
Olamilekan ya ce suna siyarwa 'yan canji da jabun kudin waje yayin da matarsa ke rabawa kwastamoni jabun naira ta san'ar POS.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng