An Nemi Binciken 'Dan Majalisa kan Zargin Ba Shugaban Majalisa Cin Hancin $1.7m

An Nemi Binciken 'Dan Majalisa kan Zargin Ba Shugaban Majalisa Cin Hancin $1.7m

  • Wasu kungiyoyi 72 sun yi kira da a gaggauta binciken dan majalisa bisa zargin bayar da cin hanci ga shugaban majalisar
  • Ana zargin Hon. Ugochinyere Ikenga ya ba da cin hancin Dala Miliyan 1.7 ga Rt. Hon Tajudeen Abbas domin samun mukami
  • Ikenga ya musanta cewa akwai wannan magana, inda ya misalta ta da wasan kwaikwayo da wasu barayin fetur su ka hada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Kungiyar Arewa ta Northern Stakeholders Consultative Forum ta bukaci mahukuntan kasar nan su gaggauta binciken dan majalisa, Hon. Ugochinyere Ikenga.

Wannan na zuwa ne bayan zargin da ake yiwa dan majalisa Ikenga na mika cin hancin makudan daloli ga shugaban majalisa, Rt.Hon Tajjudeen Abbas.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Majalisa
Ana zargin cin hancin Dala Miliyan 1.7 ya gifta tsakanin mamba da shugaban majalisa Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa ana zargin Hon. Ikenga da neman cin hanci, da kurarin ya ba wa shugaban majalisa Rt. Hon. Abbas $1.7m domin nada shi shugaban kwamitin man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyi sun nemi zurfafa bincike a majalisa

Kungiyar Northern Stakeholders Consultative Forum ta jagoranci wasu kungiyoyi 72 wajen mika bukatar binciken zargin cin hanci tsakanin dan majalisa Ikenga da shugaban majalisa.

Jaridar Leadership ta wallafa cewa dan majalisar ya musanta zargin, inda ya ce wasan kwaiwayo ne kawai da wasu barayin fetur su ka kitsa saboda tsoron a bibiyesu.

Amma kungiyoyin sun ce Ikenga da ke wakiltar Ideato ta Arewa da Kudu a jihar Imo na cikin zargi, saboda haka ta a duba kyamarar CCTV ta majalisa domin tabbatar da zargin da ake yi.

An fara binciken dan majalisa kan cin hanci

Kara karanta wannan

Matasa miliyan 1 za su yi tattakin goyon bayan Tinubu bayan zanga zangar adawa

A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun Abuja ta sahalewa hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta binciki dan majalisar da ya fi kowa dadewa a majalisa, Nicholas Mutu.

Ana zargin Hon. Mutu da wawashe kudin kwamitin da ya jagoranta na NDDC a lokacin da ya shugabance shi, inda ake zarginsa da badakalar Naira Miliyan N320m da tallafin wani kamfani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.