A karo na 6, NNPCL Ya Karya Alkawarin da Ya Dauka a kan Gyara Matatar Ribas

A karo na 6, NNPCL Ya Karya Alkawarin da Ya Dauka a kan Gyara Matatar Ribas

  • Bayan sanya ranar fara aiki har sau shida, matatar man kamfanin NNPCL ya gagara fara aiki a watan da hukumomin kasar nan su ka ce zai fara tace fetur
  • A watan Yulin 2023 ne shugaban kamfanin man na kasa, Mele Kyari ya dauki alkawarin cewa matatar da ke jihar Ribas za ta fara aiki a farkon watan Agusta
  • Wannan ba shi ne karon farko da hukumomin kasar nan ke gaza cika alkawarin farfado da matatan man da ake da su ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers - Matatar man fetur ta Fatakwal da ke jihar Ribas ta gaza fara aiki a watan nan duk da alkawarin da shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya dauka.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Ma'aikatar albarkatun man fetur ta kasa da kamfanin man fetur sun dade su na shaidawa 'yan kasar nan cewa matatun cikin gida da ake da su na dab da fara tace fetur.

Frederico Parra
Duk da alkawuran kamfanin NNPCL, matatar Fatakwal ta gaza fara aiki Hoto: Frederico Parra
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa a shekarar 2023, Mele Kyari ya bayyana cewa an kusa kammala aikin matatar fetur ta Fatakwal, kuma za ta fara aiki a farkon watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana fargabar aikin matatar Fatakwal ya tsaya

Bayan yadda matatar fetur din fatakwal ta gaza fara aiki zuwa yanzu, an shiga zulumin wannan karon ma aikin matatar ya tsaya cak kamar yadda aka yi a baya, The Cable ta wallafa.

Ko a shekarar 2019, Mele Kyari ya bayyana cewa dukkanin matatun fetur din cikin gida za su fara aiki kafin karshen wa'adin shugaba Muhammadu Buhari da ya kare a 2023.

Kara karanta wannan

Matatar man Dangote za ta sayar da litar fetur a kan N600? Kamfanin ya yi karin haske

Matatar Dangote ta fayyace gaskiyar farashin fetur

A wani labarin kun ji cewa matatar man Dangote ta bayyana gaskiyar batun da 'yan kasuwar man fetur a kasar nan su ka yi na cewa an kayyade farashin fetur dinsa a kan N600.

Shugaban sashen sadarwa na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ya bayyana cewa sun samu labarin da aka wallafa a kan kayyade farashin, kuma ba gaskiya ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.