Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Hanyar da Za a Iya Raba Tinubu da Mulkin Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Hanyar da Za a Iya Raba Tinubu da Mulkin Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta yi martani kan masu yin kira da a canza gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Ministan ma'adanai, Dele Alake, ya ba su shawara da su jira sai zuwa lokacin zaɓen 2027 domin su cimma wannan manufa
  • Alake ya bayyana cewa zanga-zangar nan da aka yi, wani yunƙuri na ganin an canza gwamnatin Tinubu a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shawarci masu kiran da a canza gwamnati su jira har sai zuwa lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ministan ma’adanai na ƙasa, Dele Alake ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa.

Gwamnatin tarayya ta gargadi masu son a canza gwamnati
Shugaba Tinubu ya jagoranci taron majalisar magabata Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Dele Alake ya bayyana hakan ne bayan kammala taron majalisar magabata ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Dan Bello ya sake kwancewa gwamnatin Tinubu zani a kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi yunƙurin canza gwamnatin Tinubu

Alake ya ce zanga-zangar yunwa da aka gudanar a baya-bayan nan wani yunƙuri ne na canza gwamnati da ƙarfin tuwo wanda kuma aka bijire masa, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa majalisar ta godewa ƴan Najeriya kan yadda suka bijirewa yunƙurin na canza gwamnati ba ta hanyar da ta dace ba.

"Ina kiransa yunkuri ne na ƙoƙarin canza gwamnati ta ƙarfin tsiya wanda kuma aka bijire masa. Majalisar ta godewa ƴan Najeriya kan yadda suka bijirewa yunƙurin canza gwamnati ta hanyar da ba ta dace ba."
"Idan akwai wanda bai gamsu da gwamnati ba, ko gwamnati mai ci, akwai lokacin zuwan zaɓe, domin haka sai ya jira zaɓe sannan ya kaɗa ƙuri’a."
"Duk wani canjin gwamnati dole ne ya kasance ta hanyar zaɓe ba ta hanyar bindiga ba, ko ta hanyar tayar da ƙayar baya ko ta wata hanya da ta saɓawa kundin tsarin mulki. Ta hanyar akwatin zaɓe ne kaɗai za a iya canza kowace gwamnati."

Kara karanta wannan

"Yana da kyakkyawan shiri": Hadimin Tinubu ya kwantar da hankalin matasan Najeriya

- Dele Alake

Majalisa ta gamsu da mulkin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar magabata da suka hada da Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da gwamnatin Bola Tinubu a ranar Talata 13 ga watan Agusta.

Majalisar ta bayyana gamsuwarta da yadda gwamnatin Tinubu ke gudanar da ayyukanta bayan ta saurari jawabin ministoci shida da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng