Ministan Makamashi Ya Yi Albishir, Ya Fadi Dalilin Karuwar Wuta a Ƙasa

Ministan Makamashi Ya Yi Albishir, Ya Fadi Dalilin Karuwar Wuta a Ƙasa

  • Ministan hasken wutar lantarki, Injiniya Adebayo Adelabu ya bayyana cewa ana samun karuwar hasken wutar lantarki a kasar nan
  • Adelabu ya ce gwamnati ta dauki matakai, kuma ana cigaba da samar da wasu tsare-tsaren inganta rarraba hasken wuta ga 'yan kasa
  • Gwamnatin Bola Tinubu ta san muhimmancin wutar lantarki ga sauran sassan cigaba, shi yasa ake daukar matakan wadata kasa da haske

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Cross Rivers - Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa yanzu wuta ta kara samuwa a sassan kasar nan biyo bayan shirin gwamnati.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sanya wasu matakai da za su tabbatar da wadatar hasken wutar lantarki a kasa.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Adebayo
Ministan lantarki ya ce ana samun karuwar wutar lantarki a kasar nan Hoto: Hon. Adebayo Adelabu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Injiniya Adelabu ya fadi haka ne lokacin da ya kai ziyara tashar rarraba hasken wuta ta Calabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya kara da cewa tashar ta Calabar ce ta fi dukkanin tashoshin rarraba hasken wuta biyar da ake da su a kasar nan, kuma za a tabbata hakan ya dore.

"Gwamnatin Tinubu ta san muhimmancin lantarki," Minista

Ministan makamashin, Adebayo Adelabu ya bayyana muhimmancin da samar da wadataccen hasken wuta ke da shi a kasa.

Ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta san da hasken wuta sauran bangarorin cigaban kasa su ka dogara, saboda haka ne aka rubanya kokari domin samar da ita.

Injiniya Adelabu ya kara da cewa gwamnati ba za ta rika wasa da samar da hasken lantarki ga 'yan kasar ba kamar yadda ake a baya.

Kara karanta wannan

Majalisar magabata: Buhari, Jonathan sun magantu kan yadda Tinubu ke mulkin Najeriya

Ministan Tinubu ya yi albishir kan lantarki

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen magance matsalolin da su ka addabe bangaren wutar lantarki.

Ministan wutar makamashi, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa kudurin lantarki na shekarar 2023 zai ba wa yan kasa damar samun wadataccen wuta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.